Tsaro a Abuja: Majalisar Dattijai Za Ta Gayyaci Wike da Wani Minista, In Ji Sanata Kingibe

Tsaro a Abuja: Majalisar Dattijai Za Ta Gayyaci Wike da Wani Minista, In Ji Sanata Kingibe

  • Majalisar Dattijai za ta gayyaci ministan FCT, Nyesom Wike da wasu jami'an tsaro domin su ba da rahoto kan matsalar tsaro a Abuja
  • Yar majalisa mai wakiltar FCT, Sanata Ireti Kingibe ta sanar da hakan inda ta ce ta dade tana ankarar da Wike kan matsalar tsaron
  • A baya-bayan nan dai an samu yawaitar hare-haren 'yan bindiga da kuma sace mutane a babban birnin tarayya Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Sanata Ireti Kingibe ta ce Majalisar Dattijai za ta gayyaci ministan babban birnin tarayya (FCT) Nyesom Wike da hukumomin tsaro kan yawaitar 'yan ta'adda a babban birnin kasar.

A yayin da hare-haren 'yan bindiga ya fara kamari a Abuja, 'yar majalisar mai wakiltar FCT ta ce idan majalisar ta dawo hutu a watan nan, za ta yi zama da ministan don jin shirinsa na tabbatar da tsaron yankin.

Kara karanta wannan

An yi wa shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage, fashi a Landan

FCT: Majalisar dattijai za ta gayyaci Wike da wani minista
Rashin tsaro a FCT: Wike da wani minista za su gurfana gaban majalisar dattijai, Inji Sanata Kingibe. Hoto: @IretiKingibe, @GovWike
Asali: Facebook

Majalisar dattawa za ta gana da Wike da jami'an tsaro

Sanata Kingibe, wadda aka zaba a karkashin Jam’iyyar Labour (LP) ta bayyana hakan a cikin wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shafin gidan talabijin din ya ruwaito Sanata Ireti Kingibe na cewa:

“Da zaran Majalisar Dattijai ta dawo daga hutu, kwamitin babban birnin tarayya, zai gana da ministocin biyu da jami’an tsaro domin su ba mu tsare-tsarensu kan tsaron yankin.
"Amma ko ya amsa gayyatar majalisar ko ya ki amsawa ba wani lamari ne na daban. Amma a matsayinsa na babban jami’in tsaro na FCT ya kamata ace yana da wani shiri da ya yi."

A gano bakin zaren matsalar don yi wa tufkar hanci

‘Yar majalisar da ta karbi mukaminta a shekarar da ta gabata ta yabawa jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dakile miyagun laifuka a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Satar mutane a Abuja: "Mun kama wasu masu yiwa yan bindiga leken asiri", Wike ya yi karin bayani

Sai dai ta ce tun kafin al’amura su yi zafi, ta yi ta kokarin ankarar da Wike kan rashin tsaro a Abuja.

"Na yi kokarin jawo hankalinsu sai aka ce mini na faye yin raki da yawa, ni kuma na ce ba haka ba ne saboda abin da nake fada masu na fitowa ne daga bakin 'yan mazabata.
"Akwai babban aiki a gaban mu, domin kama masu garkuwar ba shi ne mafita ba, dole mu gano bakin zaren lamarin don yi wa tufkar hanci gaba daya."

A cewar Sanata Kingibe.

Gwamnatin Jigawa ta dakatar da jami'ai 28, an gano dalili

A wani labarin, gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya ba da umurnin dakatar da shugaban shirin Fadama III na jihar tare da wasu jami'ai 27, saboda karkatar da naira biliyan 1.7.

An ruwaito cewa a shekarar 2022 gwamnatin jihar ta wakilta wadanda aka kora da su raba tallafin COVID-19 ga marasa galihu a jihar, amma suka karkatar da kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel