Masu Garkuwa da Mutane Sun Kai Hari Rukunin Gidajen Sojoji a Abuja, Sun Sace Mutane

Masu Garkuwa da Mutane Sun Kai Hari Rukunin Gidajen Sojoji a Abuja, Sun Sace Mutane

  • A daren ranar Alhamis ne mazauna rukunin gidajen sojoji da ke Abuja suka shiga tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka farmake su
  • An ruwaito cewa misalin karfe 10 na dare 'yan bindigar suka bude wuta unguwar da ke Phase 2, kuma sun yi awon gaba da mutum biyu
  • Duk da cewa sojoji sun kai daukin gaggawa amma sun makara, domin kafin su karasa tuni 'yan bindigar suka gama aiwatar da danyen aikin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wasu masu garkuwa da mutane sun kai hari a rukunin gidajen sojojin Najeriya da ke Abuja a daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da mutane biyu.

Kara karanta wannan

Basaraken Abuja da aka yi garkuwa da shi a 2023 ya kubuta, an biya naira miliyan 8 kudin fansa

Lamarin ya faru da misalin karfe 10 na dare a unguwar Phase 2 , inda masu garkuwan suka sace wata mata da daya daga cikin surukan wani Barista Cyril Adikwu.

Yan bindiga sun kai hari rukunin gidajen sojoji a Abuja
Yan bindiga sun kai hari rukunin gidajen sojoji a Abuja, sun sace mutane. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Yadda 'yan bindigar suka farmaki rukunin gidajen

A cewar Austine John, makwabcin Barista Adikwu, masu 'yan bindigar sun fara harbe-harbe a lokacin da suka shiga gidan Adikwu, suka sace mutanen amma shi ya tsere, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mr John ya ce:

"Misalin karfe 10 na dare muka fara jiyo karar harbe-harben bindiga, da hanzari na fita don tabbatar da kofar gidana a rufe take, don mun san ba lafiya.
"Sun shiga gidan Barista, muka sanar da hukumar gudanarwar rukunin gidajen, wadanda suka dauki matakin gaggawa. Sojoji sun zo sun fara harbi su ma, amma tuni an tafi da mutanen."

An roki Tinubu ya kawo karshen 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan sanda sun ceto wani mutum da aka sace a Abuja, an kama mai garkuwan

Jaridar Platinum Times ta ruwaito Mr John ya ce tsawon wannan dare ba su yi bacci ba saboda tsoron 'yan bindigar na iya dawowa don sake tafiya da wasu.

Ya roki shugaban kasa Bola Tinubu da ya kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a Abuja da ma Najeriya baki daya, wanda ke kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Yan bindiga sun saki basaraken Abuja bayan karbar N8m

A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun saki basaraken Abuja da mukarrabansa biyar da suka sace tun a watan Disamba 2023.

Rahotanni sun bayyana cewa sai da aka biyan naira miliyan takwas kudin fansa kafin aka sako basaraken da mukarrabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel