Tinubu, Shettima da Gwamnoni Sun Dira Ibadan Don Taya Akande Murnar Cika Shekera 85
- Garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo ya yi cikar kwari yayin da tsohon shugaban APC na kasa, Bisi Akande ya cika shekaru 85
- Tuni manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya suka fara hallara a cibiyar taro na kasa da kasa da ke jami'ar Ibadan don taya shi murna
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda aka wakilta, mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni duk sun hallara
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Manyan jiga-jigan Najeriya sun fara isa cibiyar taro na kasa da kasa da ke jami'ar Ibadan, domin taya tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande, murnar cika shekaru 85 a duniya.
Betta: Gbajabiamila ya amince da N2bn ba tare da izinin Tinubu ba? Fadar shugaban kasa ta yi martani
Yayin taron an kuma tsara za a kaddamar da wata gidauniya ta Adebisi Akande, rahoton The Nation.
Haka kuma za a yi gudanar da wata makabala kan shugabanci karkashin jagorancin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin manyan bakin da suka fara halartar wajen sun haɗa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu ya wakilta.
Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima, da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum.
An tsara taron rukuni-rukuni, inda aka zabi shugaban kasa da mataimakinsa su tsaya a matsayin manya baki a wajen, kuma Kashim Shattima na daga cikin masu gabatar da jawabi.
Su wanene suka halarci taron?
Sauran gwamnonin da suka halarci wajen sun haɗa da na Ogun Dapo Abiodun, na Ekiti Abiodun Oyebanji, da na Osun Ademola Adeleke.
Akwai ministocin Tinubu da suma sun hallara a wajen da suka haɗa da ministan makamashi, Cif Adebayo Adelabu da takwaransana tattalin arziki Adegboyega Oyetola da sauran manyan baki, rahoton Vanguard.
Tinubu ya hadu da Obasanjo a Imo
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo a baya cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo sun hadu a wajen rantsar da Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo.
An dai rantsar da Uzodimma ne a matsayin gwamnan jihar Imo a karo na biyu a garin Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.
Wannan ita ce karo na farko da shugabannin biyu ke haduwa tun bayan babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng