Hukumar EFCC Ta Cafke Halima Shehu Shugabar Hukumar NSIPA Bayan Shugaba Tinubu Ya Dakatar da Ita

Hukumar EFCC Ta Cafke Halima Shehu Shugabar Hukumar NSIPA Bayan Shugaba Tinubu Ya Dakatar da Ita

  • An cafke Halima Shehu, shugabar hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA) da Shugaba Tinubu ya dakatar
  • An tattaro cewa hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta kama ta a ranar Talata, 2 ga watan Janairu
  • Rahotanni sun bayyana cewa kama ta na da nasaba da badaƙalar Naira biliyan 37.1 da aka tafka a gwamnatin da ta shuɗe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), ta cafke Halima Shehu, dakatacciyar shugabar hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA).

Wannan kame dai wani ɓangare ne na binciken da ake yi na karkatar da wasu maƙudan kuɗade N37,170,855,753.44 a ma’aikatar kula da jin ƙai a zamanin tsohuwar minista Sadiya Umar-Farouk, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yi wa Sadiya Farouk tambayoyi kan zargin karkatar da N37bn a gwamnatin Buhari

Hukumar EFCC ta yi caraf da Halima Shehu
Hukumar EFCC ta cafke Halima Shehu, dakatacciyar shugabar hukumar NSIPA Hoto: Halima Shehu, EFCC Nigeria
Asali: Facebook

A ranar Talata da misalin ƙarfe 9:00 na safe jami’an hukumar EFCC sun kai samame ofishin NSIPA da ke sakatariyar gwamnatin tarayya a babban birnin tarayya Abuja, inda daga bisani suka tafi da Halima hedikwatar EFCC da ke Jabi Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zuwa daren Talata, an tattaro cewa hukumar ta cigaba da tsare ta kuma tana fuskantar tambayoyi.

Meyasa EFCC ta cafke Halima Shehu?

Majiyoyi daga manyan jami’ai daga hukumar EFCC sun bayyana cewa Halima tana da hannu a cikin badaƙalar kuɗi biliyan 37.1 a lokacin da take riƙe da muƙamin tsohuwar kodinetan shirin bayar da tallafin kuɗi a ƙarƙashin ma’aikatar.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, majiyar ya bayyana cewa:

"A halin yanzu Halima Shehu tana hannunmu (EFCC) kan badaƙalar N37.1bn da aka yi a zamanin tsohuwar ministar jin ƙai, Sadiya Umar-Farouk.
"Halima ita ce kodineta ta ƙasa mai kula da shirin bayar da tallafin kuɗi na ma’aikatar a zamanin Buhari, kuma an yi mata tambayoyi kan wasu kuɗaɗen da suka bar asusun ma’aikatar ta hannunta."

Kara karanta wannan

Cikakken jerin jami'o'in kasashen waje da gwamnatin Tinubu ta haramta a Najeriya

A ranar Talata, 2 ga watan Janairun 2024, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da Halima Shehu daga mukaminta.

Shugaba Tinubu Ya Maye Gurbin Halima Shehu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon shugaban hukumar NSIPA, bayan ya dakatar da Halima Shehu.

Shugaban ƙasa ya naɗa dakta Akindele Egbuwalo, a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan Halima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel