An Kama Wata ‘Kwararriyar’ Barauniyar Waya da Wasu Mutum 84 a Borno, Ta Bayyana Yadda Ta Ke Takunta

An Kama Wata ‘Kwararriyar’ Barauniyar Waya da Wasu Mutum 84 a Borno, Ta Bayyana Yadda Ta Ke Takunta

  • 'Yan sanda sun cafke wata wata wacce ta kware wurin sata da kwacen waya a birnin Maiduguri
  • Wacce ake zargin mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' an cafke ta ne tare da wasu mutane 84 kan zargin wasu laifuka
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Daso Nahum ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis 4 ga watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta cafke wata mata kwararriyar mai kwacen waya a Maiduguri.

Wacce ake zargin mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' ta shiga hannu da wasu mutane 84, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta kori jami'anta 2 daga aiki, za ta gurfanar da su gaban kotu, ta fadi dalili

'Yan sanda sun cafke wata kwararriyar mai kwacen waya a Borno
An Kama Wata ‘Kwararriyar’ Barauniyar Waya a Borno. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene ake zargin matar da aikatawa a Borno?

Sauran mutanen da aka kaman ana zarginsu da aikata laifuka da dama da suka hada da mallakar makamai da fashi da kisan kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin gabatar da masu laifin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Daso Nahum ya ce sun aikata da laifukan ne daga 1 ga watan Oktoba zuwa 31 ga watan Disamba.

Nahum ya bayyana haka ne a jiya Alhamis 4 ga watan Janairu a Maiduguri babban birnin jihar, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Mene rundunar ta ce kan wacce ake zargin?

Kakakin ya ce Bintu wacce ke zaune a unguwar Shehuri a cikin Maiduguri ta shiga hannu a ranar 28 ga watan Disamba.

Ya ce:

"Yayin binciken Bintu ta bayyana sunan wani Mohammed Isa da ke Babban Layi da suke harkar tare.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama fasto da wasu mutane biyu kan damfara a Kogi

"Yadda su ke aikata satar shi ne zuwa gidajen mutane a matsayin masu aiki inda suke sace wayoyinsu."

Tirela ta murkushe sabon dan sanda a Jigawa

A wani labarin, wani matashin dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan tirela ta murkushe shi a jihar Jigawa.

Marigayin mai suna Abba Safiyanu an tabbatar da cewa sabon shiga aikin dan sanda ne wanda aka tura jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Ringim da ke jihar a ranar Talata 2 ga watan Janairu da yammacin ranar ta wannan mako da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.