Manyan Shari’o’i 5 Da Aka Gagara Kai Karshensu a Shekarar 2023

Manyan Shari’o’i 5 Da Aka Gagara Kai Karshensu a Shekarar 2023

  • Shekarar 2023 ta kare da batutuwa da dama da gwamnatin tarayya ba ta warware ba a dukkan matakai
  • Akwai shari'o'i tsaffi da saffi da aka fara su a 2023 ba a kammala ba, wata kila sai a wannan shekarar ta 2024
  • Legit ta yi nazarin wasu manyan shari'o'i guda biyar da suka ja hankali a 2023 kuma ba a iya an kammala su ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abubuwa da dama sun faru a Najeriya da suka dauki hankali a shekarar 2023 da ta shude, ciki kuwa har da fannin shari'a, wanda za mu yi magana yanzu a kansa.

Kama daga siyasa, zuwa cin hanci da rashawa da sauran laifuka, Hukumomin tsaro sun shigar da kararraki daban-daban gaban manyan kotunan kasar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, sun sace fasinjojin da suka tafi hutun Kirsimeti

Shari'o'i 5 da ba a kamalla su a 2023 ba
Legit ta yi nazarin wasu manyan shari'o'i guda biyar da suka ja hankali a 2023 kuma ba a iya an kammala su ba. Hoto: Godwin Emefiele, Abba Kyari
Asali: UGC

A yayin da aka warware wasu, wasu kuma har shekarar ta kare ba a iya an kammala su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta yi nazari kan wasu manyan shari'o'i 5 da aka gagara kai karshen su a 2023.

Shari'ar DCP Abba Kyari

A ranar 14 ga Fabrairu, 2022, aka kama jami’in dan sanda DCP Abba Kyari tare da tuhumarsa shi da laifuka da dama da suka shafi safarar miyagun kwayoyi da safarar kudade.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kuma zarge shi da kasancewa cikin kungiyar masu safarar hodar Iblis daga Brazil zuwa Habasha da Najeriya.

A watan Yulin 2023, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belinsa a wata shari’ar da ke da alaka da rashin bayyana kadarorinsa, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Rundunar Sojojin Najeriya ta kama jami’inta kan mutuwar direban babban mota a Borno

Tsohon akanta janar na tarayya, Ahmed Idris

Hukumar EFCC ta kama tsohon akanta janar na tarayya, Ahmed Idris a watan Mayun 2022 bisa zargin karkatar da kusan dala miliyan 200 (N109bn) na dukiyar al’umma.

Kotu ta bayar da belinsa a watan Yulin 2022, amma tare da wasu sharudda masu tsauri, kamar ajiye naira miliyan 500, mika fasfo dinsa da kuma kai rahoto ga EFCC sau biyu a mako.

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele

A cikin watan Yunin 2023, DSS ta kama tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, bisa zargin mallakar bindiga da kuma daruruwan harsashi ba bisa ka'ida ba.

A watan Yulin 2023, gwamnatin tarayya ta shigar da kararrakin tuhume-tuhume har guda 20 a kansa, inda ta zarge shi da laifin hada baki, damfarar sayayya, halasta kudaden haram, da kuma cin zarafin ofis.

A ranar 8 ga Nuwamba, 2023, mai shari’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya ysa bayar da belinsa.

Kara karanta wannan

Mafi munin sata da rashin gaskiyar da aka yi a lokacin mulkin Buhari

Tsohon shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa

A ranar 14 ga watan Yunin 2023, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar Ahmed Bawa daga mukamin shugaban hukumar EFCC tare da umurtar hukumar SSS ta tsare shi domin yi masa tambayoyi.

An zarge shi da laifuffuka da dama, kamar cin zarafi, cin hanci da rashawa, da kuma raina kotu. Hukumar SSS ta tsare shi sama da watanni biyu, har sai a ranar 25 ga Oktoba, 2023 ta sake shi.

Tsohon MD, kamfanin KASCO na jihar Kano, Bala Inuwa

Ana zargin Bala Muhammad Inuwa, tsohon MD na kamfanin samar da kayan noma na jihar Kano (KASCO) da karkatar da sama da naira biliyan hudu.

Ya fitar da kudin ne daga asusun gwamnatin jihar zuwa asusun sa da na dansa Bala Muhammad Inuwa Junior da kungiyar abokansa.

Wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su, inda suka nemi a bayar da belinsu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta fara tuhumar wasu manyan ministocin Buhari kan badakalar naira biliyan 187

Yan bindiga sun sake afkawa kauyen Neja, sun sace Mata da miji

A wani labarin, wasu gungun 'yan bindiga sun sake kai farmaki kauyan Garam a jihar Neja da ke da makwabtaka da Abuja inda suka sace mutum uku.

An ruwaito cewa, 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, kuma sun yi nasarar awon gaba da mata da miji da karamin yaron da ke zama tare da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel