Yanzu-Yanzu: An Kama Akanta-Janar Na Tarayyar Najeriya, Ahmed Idris

Yanzu-Yanzu: An Kama Akanta-Janar Na Tarayyar Najeriya, Ahmed Idris

  • Jami'an Hukumar EFCC sun kama Akanta-Janar Na Tarayyar Najeriya, Ahmed Idris a Kano bisa zarginsa da hannu cikin badakalar Naira Biliyan 80
  • Bayan kama Idris, jami'an na EFCC sun dauke shi a jirgin sama an nufi birnin tarayya Abuja domin su kai shi ofishinsu ya amsa tambayoyi
  • Majiyoyi daga EFCC sun tabbatar da kama Idris suna mai cewa an dade ana gayyatarsa zuwa amsa tambayoyi kan binciken amma ya ki zuwa hakan ta sa dole aka kama shi

Jaridar Premium Times ta ce ta samu sahihin rahoto da ke tabbatar da cewa an kama Akanta Janar na tarayyar Najeriya, Ahmed Idris, kan zargin almundahanar kudi da karkatar da kudin gwamnati.

Wadanda suke da masaniya kan lamarin sun ce jami'an EFCC na Kano ne suka kama Idris a yammacin ranar Litinin kuma za a tafi da shi Abuja domin amsa tambayoyi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ranar Litnin za'a dawo jigilar mutane a jirign kasan Abuja-Kaduna, Gwamnatin tarayya

Yanzu-Yanzu: An Kama Akanta-Janar Na Najeriya, Ahmed Idris a Kano
Jami'an EFCC Sun Kama Akanta-Janar Na Najeriya, Ahmed Idris a Kano. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

Majiyoyi sun ce EFCC ta dade tana bincike a kan zargin karkatar da Naira biliyan 80 na kudin gwamnati ta hanyar wasu kwangiloli na bogi.

Masu binciken sun ce an gano cewar kamfanonin da aka yi amfani da su wurin karkatar da kudin suna da alaka da yan uwan Akant Janar din da abokansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Premium Times ta rahoto, majiyoyi sun ce bayan an fara zurfi a binciken, an sha gayyatar Mr Idris domin ya zo ya amsa tambayoyi amma ya ki zuwa.

"Mun sha gayyatarsa amma ya ki zuwa," a cewar daya cikin majiyoyin.
"Ba mu da wani zabi sai sa masa ido sannan mu kama shi."

An yi kokarin ji ta bakin kakakin EFCC game da labarin amma daya cikin na kasa da shi ya ce ya tafi Birtaniya a yanzu.

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Amma, wani babba a EFCC ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce kada a fada sunansa domin ba a bashi izinin yin magana da manema labarai ba.

Yashe Idris ya zama Akanta Janar?

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Mista Idris matsayin Akanta Janar ne a ranar 25 ga watan Yunin 2015.

An samu gurbi a ofishin ne bayan tsohon Akanta Janar, Jonah Otunla, ya bar ofishin a ranar 12 ga watan Yunin 2015.

Shugaba Buhari ya sake sabunta nadin Idris a Yunin 2019, duk da cewa kungiyoyin kwadago sun rika korafin cewa ya kamata ya yi murabus tun da ya cika shekaru 60.

An haifi Idris ne a Jihar Kano, Arewa maso Yammacin Najeriya a ranar 25 ga watan Nuwamban 1960, kuma kafin nadinsa a 2015, shine Direktan Kudi da Asusu, Ma'aikatar Ma'adinai da Karafa.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel