Gwamnatin Abba ta Zargi Jami’in Gwamnatin Ganduje da Satar Biliyoyi a Kano

Gwamnatin Abba ta Zargi Jami’in Gwamnatin Ganduje da Satar Biliyoyi a Kano

  • Ana shari’a tsakanin wani tsohon shugaban hukumar KASCO, Bala Inuwa Muhammad da gwamnatin jihar Kano a kotu
  • Binciken PCACC ya nuna an saci kudi daga 2022 zuwa 2023 a KASCO, saboda haka gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kai shi kara
  • Babban lauyan gwamnatin Kano ya na tuhumar Bala Inuwa Muhammad da karkatar da N4bn da kuma bada cin hanci a ofis

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta tuhumi tsohon shugaban hukumar KASCO, Bala Inuwa Muhammad, da zargin satar Naira biliyan 4.

Rahoto ya fito daga Premium Times cewa ana zargin Bala Inuwa Muhammad da yaronsa da wasu mutum biyu kamfaninsa da satar kudi.

An shigar da karar a kotu ne ta ofishin Babban lauyan gwamnatin jihar Kano a sakamakon korafin da aka samu daga hukumar PCACC.

Gwamnatin Abba
Gwamnan Kano ya yi bincike a KASCO Hoto:Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tsohon shugaban KASCO ya kalubalanci hurumin PCACC

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabbin Shugabanni Biyu a Ma’aikatar Lafiya

Bayanan da jaridar ta samu sun tabbatar da cewa karar ta na gaban wata babban kotun jihar Kano ne a teburin Mai shari’a Hafsat Sani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda ake kara sun dauki lauya ana kalubalantar hurumi, su na cewa hukumar PCACC ba ta da ikon yin binciken har a shigar da kara.

Gwamnatin Kano ta ja da ikirarin nan a kotu, kuma ta roki Alkalai su yi watsi da shi domin tun can an kafa PCACC a doka ne saboda irin haka.

A hukuncin da kotu ta fara gabatarwa, ta ce hukumar ta na da ikon yin bincike, ta kama wanda ake zargi, kuma a iya shigar da kara a kotu.

Gwamnatin Abba za ta yi shari'a da Bala Inuwa Muhammed

Wannan hukunci zai bada damar sauraron shari’ar mai lamba K/154C/2023 tsakanin gwamnati Bala Inuwa Muhammed da wasu mutum hudu.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu Ya Amince Da Nadin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa

Ana zargin Bala ya karkatar da N3.2bn da N480m daga asusun KASCO zuwa kamfanin Limestone Processing Links da ake zargin na sa ne.

Gwamnati ta ce tsohon jami’in ya aikawa wasu ma’aikatan jihar Kano cin hancin N15m saboda a rufe maganar, an yi haka ne a 2022 da 2023.

Tsohon Kwamishina ya yi murabus

Rahoton da mu ka samu a baya ya nuna ana zargin wanda Gwamnan Sokoto ya nada domin magance rashin tsaro da alaka da ‘Yan bindiga.

Rade-radin nan su na fara yawo aka ji Kanal Garba Moyi Isa ya ajiye mukaminsa, ya ce babu abin da zai jawo ya saida mutuncinsa kan duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel