Amfanin Mangwaro guda 6 a jikin dan Adam

Amfanin Mangwaro guda 6 a jikin dan Adam

- Allah ya sanya tarin alfanu ga yayan bishiya musamman kayan marmari

- Shima Mangwaro nada tarin sinadarai masu amfani sosai ga jikin dan Adam

Wato jama’a da dama sukan sha mangwaro ne kawai ba tare da sanin menene asalin amfaninsa ga jikkunansu ba, asali ma wannan shi yasa birai ke kaunar shan mangwaro.

Ba za’a ga laifin su idan aka yi duba ga zakin da mangwaro yake da shi, musamman idan mutum ya samu binta siga, ko yar kamaru ko kuma mai warin gawasa, kaga kuwa duk mutumin dake yin karo da irin wannan mangwaron akai akai, ai sai dai a kyale shi aya more.

KU KARANTA: Dangote ya sayar da kamfanin sarrafa Noodles

Kamar yadda aka saba Legit.ng ba tayi kasa a gwiwa ba, ina ta kawo muku wasu alfanun Mangwaro ga dan adam guda 6, kamar haka:

1- Maganin ciwon daji (Kansa)

Bincike da kwararru suka gudanar ya tabbatar da cewa mangwaro na dauke da sinadarai kamar su ‘quercetin, isoquercitrin, astragalin, fisetin da gallic acid’ wadanda suke maganin ciwon daji, musamman muggan ciwukan da suka shafi nono, mara da kuma sikila.

Amfanin Mangwaro guda 6 a jikin dan Adam
Mangwaro

2- Rage kiba

Sakamakon kasancewar sinadarin ‘pectin da vitamin C’ a cikin mangwaro da kuma bawon mangwaron kansa, yasa mangwaro na hana mutum kiba ta hanyar narkar da kitse a jikin mutum.

3- Gyara fata

Idan kana so fatar ka tayi kyau, tana kyalli tana sheik, musamman ga yan mata, toh kid age da shan mangwaro, saboda sinadaran dake cikinta suna gyara fata tare da maganin kurajen fuska.

4- Kara lafiyan Ido

Masana sun tabbatar da kasantuwar sandarin ‘Vitamin A’ dake gyara ido a cikin mangwaro, don haka mangwaro na kara karfin gani, kuma yana maganin bushewar idanu.

Amfanin Mangwaro guda 6 a jikin dan Adam
Yankakken Mangwaro

5- Kara karfin garkuwar jiki

Yawan shan mangwaro na kara ma mutum karfin garkuwar jikinsa masu yakar cututtuka a jikinsa, ba komai ya sanya mangwaro zamantowa haka ba illa tarin sinadarin ‘Vitamin C’ dake a cikinsa.

6- Taimakawa wajen nika abinci

Mangwaro na duake da wasu sinadari masu matukar muhimmanci dake taimakawa wajen nika duk abincin da mutum yaci, da wanke cikin kansa. Sanadiyyar haka mutum ba zai yi fama da rudewar ciki ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yan kasuwa sun kuka kan cinikin kayan marmari

Asali: Legit.ng

Online view pixel