Aisha Yesufu ta bada shawarar 'Yan ta'addan kungiyar IPOB su hada-kai da Jam’iyyar APGA

Aisha Yesufu ta bada shawarar 'Yan ta'addan kungiyar IPOB su hada-kai da Jam’iyyar APGA

  • Aisha Yesufu ta ba ‘Yan kungiyar IPOB shawara su hada-kai da Jam’iyyar APGA a yankin Kudu maso gabas.
  • ‘Yar gwagwarmayar tace IPOB za ta iya amfani da farin jininta, ta rika juya akalar siyasar yankin.
  • Yesufu ta na ganin zai fi kyau kungiyar ta shiga siyasa da kyau, ta daina tilastawa mutanen Ibo kulle.

Nigeria - Aisha Yesufu tayi kira ga kungiyar tsageru na Indigenous People of Biafra ta hada-kai da jam’iyyar hamayya ta All Progressives Grand Alliance.

Shahararriyar ‘yar gwagwarmayar ta bukaci ‘yan IPOB da jam’iyyar ta APGA su hada-kansu domin su dunkule mutanen yankin kudu maso yamma.

Aisha Yesufu tace a maimakon IPOB ta rika bata lokacinta wajen bada umarnin kowa ya zauna a gida, ya kamata ta maida hankali wajen samun kuri’u.

Punch ta rahoto Yesufu tana ba kungiyar tsagerun shawarar tayi amfani da muryar da farin jininta wajen ganin ‘yan takara masu nagarta sun ci zabe.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Manya-manyan ‘Yan siyasa 5 da suka fi kowa cin ribar nasarar APGA

Wannan Baiwar Allah tayi wannan magana ne bayan ganin sakamakon zaben jihar Anambra da Farfesa Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya yi nasara.

Aisha Yesufu
Aisha Yesufu tana zanga-zangar EndSARS Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da Aisha Yesufu take cewa

“Ina ma a ce kungiyar IPOB tayi aiki da jam’iyyar APGA wajen juya siyasar Kudu maso gabas?” – Aisha Yesufu.
“Su kawo ‘yan takarar da suka dace, su lashe zabe. Su nuna mana yadda mutane masu nagarta da cancanta da kwarewa za su iya kawo canji a siyasa.”

IPOB su shiga a rika damawa da su a siyasa

Jaridar kuma ta rahoto jagorar ta tafiyar BBOG tana cewa kungiyar IPOB za ta iya amfani da karfinta wajen samun yadda ta ke so a gwamnatin tarayya.

“Tarayyar APGA/IPOB za ta iya dunkule kudu maso gabas a siyasance. A maimakon IPOB ta yi ta asarar bada umarnn kulle, sai su kawo ‘yan takara.”

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Buni, Peter Obi, Uzodinma da manyan mutane 4 da APGA ta tonawa asiri

A karshe ‘yar gwagwarmayar ta bada shawarar mutanen kudu maso gabas suyi amfani da farin jinin da suke da shi wurin samun ta-cewa a siyasar Najeriya.

Anambra: Buhari ya taya Soludo murna

A yau aka ji shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Farfesa Charles Soludo murnar lashe zaben gwamna a jihar Anambra a karkashin jam'iyyar APGA.

Shugaban kasar ya bukaci Soludo da ya hada kai da sauran mutanen jihar domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a daukacin yankin Ibo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel