Aisha Yesufu Ta Nemi a Hukunta Tinubu Kamar Yadda JAMB Ta Hukunta Mmesoma

Aisha Yesufu Ta Nemi a Hukunta Tinubu Kamar Yadda JAMB Ta Hukunta Mmesoma

  • Mai sukar gwamnati, Aisha Yesufu, ta dage cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magudi ne wajen lashe zaben shugaban kasa na 2023
  • Yesufu ta ce duba ga fallasar da Mmesoma Ejikeme ta yi na aikata zamba a jarrabawar UTME da huknta ta da JAMB ta yi, ya kamata shugaban kasa Tinubu ma ya fuskanci hukunci
  • Yar fafutukar ta fada ma magoya bayan shugaban kasa Tinubu da su tambayi kansu yadda suka ji game da zambar da Mmesoma ta aikata

Nnewi, jihar Anambra - A ranar Asabar, 8 ga watan Yuli, shahararriyar yar fafutuka, Aisha Yesufu, ta ce Mmesoma Ejikeme ta sauya sakamakon jarrabawa ne kamar yadda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a lokacin zaben watan Fabrairun 2023.

Da take rubutu a shafinta na Twitter, Yesufu ta bayyana cewa ya kamata a hukunta shugaban kasa Tinubu sannan a tsige shi daga ofis kamar yadda hukumar JAMB ta hukunta Mmesoma.

Kara karanta wannan

Ya Kamata a Bari Mmesoma Ta Samu Gurbin Karatu a Jami’a: Tsohon Ministan Buhari, Ya Fadi Dalili

Aisha Yesufu ta alakanta lamarin Mmesoma da na Shugaban kasa Tinubu
“Sako Mai Ban Tsoro”: Aisha Yesufu Ta Nemi a Hukunta Tinubu Kamar Mmesoma Hoto: Peter Obi, Bola Ahmed Tinubu, Augustine Onyekachukwu Ike
Asali: Facebook

Mmesoma Ejikeme: 'Babu hujjar aikata laifi', Aisha Yesufu

Labarai sun bayyana a safiyar Asabarm 8 ga watan Yuli, cewa kwamitin da gwamnatin jihar Anambra ta kafa sun tabbatar da cewa Miss Mmesoma ta kirkiri makin 362 da ta samu a UTME ne kamar yadda hukumar JAMB ta yi ikirari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yesufu, babbar yar gani kashenin Peter Obi na jam'iyyar Labour Party (LP), ta bayyana cewa babu wani abu da zai wanke laifi da aka aikata.

Matashiyar mai shekaru 49 ta kalubalanci wadanda ke kare nasarar Tinubu a zaben 2023 da su fada ma kansu gaskiya.

Ta rubuta:

“Mmesoma ta kirkiri sakamakon jarrabawa don zama wacce ta fi kowa yawan maki a JAMB kamar yadda Bola Ahmed Tinubu ya yi magudin zabe don zama wanda ya fi kowa yawan kuri'u.
"Hukunta mutum daya (bisa daidai) da barin mutum daya aika sako mai muni ne cewa zamba ba laifi bane amma a matakin da ka aikata shi ne.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Amarya Yar Shekara 21, Maimunatu Ta Caka Wa Angonta Wuka Har Lahira Kan Karamin Abu a Bauchi

"Ba za a taba samun hujjar aikata laifi ba.
"Idan nan gaba za ku kare magudin Tinubu, ku tambayi kanku yadda kuka ji da zambar ada Mmesoma ta aikata."

Festus Keyamo ya nemi a ba Mmesoma gurbin karatu daidai da makinta

A wani labari makamancin wannan, jigon APC, Festus Keyamo ya bayyana a ranar Asabar, 8 ga watan Yuli cewa ya kamata a bari Mmesoma Ejikeme, dalibar da ta kara maki a jarrabawarta na JAMB ta samu gurbin karatu a jami'a.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Keyamo ya ce abun da Mmesoma ke bukata a yanzu shine nasiha, gyara da kuma jagoranci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel