Dan Najeriya Ya Nuna Makudan Kudaden da Aka Tura Masa Bisa Kuskure, Ya Fadi Yadda Zai Yi Da Su

Dan Najeriya Ya Nuna Makudan Kudaden da Aka Tura Masa Bisa Kuskure, Ya Fadi Yadda Zai Yi Da Su

  • Wani matashi dan Najeriya ya garzaya soshiyal midiya don baje kolin makudan kudaden da aka tura asusun bankinsa bisa kuskure
  • Da yake nuna mamakin kudin, matashin ya ce bai yi kasuwanci da kowa ba a baya-bayan nan da har za a biya shi irin wannan kudin
  • Ya bayyana abun da zai yi da kudin har zuwa lokacin da bankinsa za su kira shi yana mai cewa babu wanda ya tuntube shi zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani matashi dan Najeriya mai suna Chim Di Ebere a Facebook, ya sanar da duniya bayan an yi kuskuren tura masa kudi N289,770 a asusun bankinsa.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a, mutumin ya wallafa hoton sakon da ya samu da ke nuna kudin da aka tura masa.

Kara karanta wannan

Yar Najeriya ta koka bayan ta bude jakar yar aiki a gida, ta ga abubuwan ban mamaki a ciki

An turawa matashi kudi bisa kuskure
An yi amfani da hoton don misali ne Hoto: Ivan Pantic, Bloomberg
Asali: Getty Images

Ya ce bai san komai game da kamfanin da ya tura masa kudin ba kuma bai yi kasuwanci da kowa ba a baya-bayan nan wanda zai sa a tura masa irin wannan makudan kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abun da Chim Di Ebere zai yi da kudin

Yayin da yake rokon duk wanda yake da masaniya kan kamfanin da ya fada masu su je bankinsu, ya sha alwashin barin kudin a asusunsa har zuwa lokacin da zai samu kira daga bankinsa. Cikakken wallafar da ya yi ya kasance kamar haka:

"Ba nawa bane!!!"
"Na samu shigar wannan kudi a daren jiya daga wani kamfani da ban san komai game da shi ba; ban yi kasuwanci da kowa ba a yan baya-bayan nan da za a biya ni irin wannan makudan kudi kuma babu wanda ya tuntube ni domin sanar da ni bayani game da wannan kudi.

Kara karanta wannan

Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano

"Don haka idan ka san wani da ke aiki da kamfanin ko wanda ya san wani da ke aiki da kamfanin, don Allah ka fada masu su je bankinsu da safen nan don tabbabatr da hada-hadar kudi da suka yi fa!!!
"Kudin zai ci gaba da kasancewa a wannan asusun har sai bankina sun kira ni. Bana son matsala wannan sabuwar shekarar."

Jama'a sun yi martani

Kelvin Chukwuemeka Steven ya ce:

"Yanzu da ka yi wannan bayan awa 24 ka aika mun sako don na fada maka abun da za ka yi da shi.
"Mitoci na ta yawo ta ko'ina a wannan lokacin."

Kazeem Ibrahim ya ce:

"Ka tura shi zuwa asusuna don gudun kada ka yi amfani da shi."

Jamiu Oluwasegun Janta ya ce:

"Wannan hada-hadar kudi na bai daya ne ka ziyarci bankinka kafin ka mayar da kudi ga kowa...wasu lokutan damfara ce."

Wata mata ta fallasa mai aikinta

Kara karanta wannan

Kyakkyawar budurwa ta fashe da kuka bayan samun kyautar N20k don ta biya kudin makaranta

A wani labarin, wata matar aure ta caccaki mai aikinta kan kwashe mata kaya ba tare da saninta ba.

Matar mai suna @brownmelarnie a dandalin X ta ce yar'uwarta ta samu kira daga mai aikinta, tana mai sanar da ita game da wani kunshi da take so a kai mata kauye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel