Kano: EFCC Ta Gurfanar da Ma'aurata Kan Handame Miliyan 410, Ta Bayyana Yadda Abun Ya Faru

Kano: EFCC Ta Gurfanar da Ma'aurata Kan Handame Miliyan 410, Ta Bayyana Yadda Abun Ya Faru

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da ma'aurata a gaban babbar kotun jihar Kano kan damfara
  • Ana zargin ma'auratan, Aisha Malkohi da Abubakar Mahmoud da hadin baki da kuma damfarar miliyan 410
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafin X a yau Litinin 11 ga watan Disamba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) na zargin wasu ma'aurata a Kano, Aisha Malkohi da mijinta, Abubakar Mahmoud kan badakalar makudan kudade.

EFCC na zargin ma'auratan da damfarar naira miliyan 410 wanda yanzu haka matar ta na hannun hukumar.

EFCC ta gurfanar da ma'auratan Kano a kotu kan badakalar miliyan 410
Ma'aurata sun shiga hannu a Kano kan badakalar miliyan 410. Hoto: EFCC Nigeria.
Asali: Twitter

Mene ake zargin ma'auratan da shi a Kano?

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Hukumar LASTMA ta kori ma'aikata biyar, ta fara binciken wasu 14

Sai dai mijin ya tsare ba a san inda ya ke ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafin X a yau Litinin 11 ga watan Disamba.

Sanarwar ta ce an gurfanar da ma'auratan ne a ranar Juma'a 8 ga watan Disamba a gaban Mai Shari'a, Aisha Mahmoud a babbar kotun jihar.

Jami'an EFCC sun kama Aisha Malkohi ce kan korafin da Farida Ibrahim da Ibrahim Abdulrahman su ka shigar.

Sun zargi Malkohi da hada baki da mijinta inda su ka damfare su kudade da nufin siyo musu da motoci da gwala-gwalai da kayan wuta daga Saudiyya.

Sanarwar ta ce:

"Hukumar EFCC ta gurfanar da Aisha Malkohi da aka fi sani da 'Ummitah Arab Money' da mijinta Abubakar Mahmoud wanda ba a san inda ya ke ba kan hadin baki da damfarar miliyan 410."

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta bayyana hukuncin da ya kamata Kotun Koli ta yanke a shari'ar jihar Kano

Wane hukunci aka yi a kotun?

Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake zargin sun musanta tuhume-tuhumen da ake musu.

Mai Shari'a, Aisha Mahmoud ta ba da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargi har sai an yi hukunci kan belin.

Daga bisani ta dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 15 ga watan Disamba don yin hukunci kan belin.

EFCC ta kame makafi kan safarar kwayoyi

A wani labarin, Hukumar EFCC ta yi nasarar cafke makafi uku kan zargin safarar kwayoyi.

Hukumar EFCC na zargin makafin guda uku kan dillancin kwayoyi daga Kano zuwa Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel