NAPTIP ta ceto mata 14 daga hannun masu fataucin mutane
- Hukumar Yaki da Masu Safarar mutane (NAPTIP) ta cafke mata 14 tare da maza biyu da ke musu jagora a filin tashin jiragen sama na Abuja
- An tsegunta wa hukumar ne cewa za'a tafi da matan zuwa kasar Saudiyya inda za suyi aikatau a gidajen al'umma, hakan yasa aka kama su don bincike
- A cikin yan kwanakin nan, hukumar tana ta samun rahotanin cin zarafin al'ummar Najeriya da ke yin aikatau a kasashen gabas ta tsakiya
Hukumar Yaki da masu safarar mutane na kasa (NAPTIP) ta ceto mutane goma sha hudu daga hannun masu safarar mutane a filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban sashin hulda da jama'a na NAPTIP, Mista Josiah Emerole ya shaida wa kamfanin dillanci labarai (NAN) a Abuje cewa wasu ne suka tsegunta wa hukumar abin da ke faruwa kana sukayi nasarar cafke mutanen.
KU KARANTA: Kotu ta dage shari'ar Dasuki har sai 22 ga watan Maris
Emerole ya kara da cewa an kama mutane goma sha hudu mata wanda shekarun su bai haura 15 - 60 ba tare da maza guda biyu wanda ke jagorantar tafiyar su zuwa kasar Saudiyya.
"A halin yanzu ba'a tantance dalilin tafiyar ta su zuwa kasar ta Saudiyya ba amma cikin yan kwanakin nan muna kara samun rahotanin yadda ake cin zarafin yan gudun hijira masu yin aikatau a kasashen gabas ta tsakiya." inji shi.
Emorole ya kuma ce hukumar za ta zurafafa bincike don gano musababin tafiyar ta su da kuma gano ainihin garuruwan da matan suke da zama.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng