Izala Ta Yi Allah Wadai da Kisan Masu Bikin Maulidi a Kaduna, Ta Tura Sako

Izala Ta Yi Allah Wadai da Kisan Masu Bikin Maulidi a Kaduna, Ta Tura Sako

  • Yayin da ake jimamin mutuwar masu Maulidi a Kaduna, kungiyar Izala ta yi martani kan iftila'in da ya faru a ranar Lahadi
  • Kungiyar ta yi Allah wadai da wannan mummunan hari inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi kwakkwaran bincike
  • Ta kuma yi addu'ar samun rahama ga wadanda su ka mutu da kuma rokon ubangiji ya bai wa masu raunaka lafiya

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kungiyar Izala ta yi martani game da harin bam da aka kai kan masu bikin Maulidi a jihar Kaduna.

Kungiyar ta yi Allah wadai da harin inda ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi kwakkwaran bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mun yi takaici, shugaban sojoji ya roki afuwa kan kisan mutum 85

Kungiyar Izala ta yi martani kan harin da sojoji su ka kai kan masu Maulidi
Izala ta yi Allah wadai kan harin bam a jihar Kaduna. Hoto: Sheikh Bala Lau.
Asali: Facebook

Mene kungiyar Izalah ke cewa kan harin?

Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Talata 5 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bala Lau ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta hukunta wadanda aka samu da laifin bayan kammala binciken nata.

Shugaban Izalar ya kuma nuna alhininsa kan wannan babbar rashi da al'ummar Musulmi su ka yi dalilin harin.

Ya jajantawa iyalan wadanda su ka rasun da kuma wadanda su ka samu raunaka.

Mene martanin sojojin kan harin?

A karshe, ya musu addu'ar samun rahama da kuma rokon ubangiji ya kiyaye na gaba.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojin Najeriya ta jefa bam kan wasu mutane da ke taron Maulidi a Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Rundunar daga bisani ta yi martani inda ta ce ta kai harin a kuskure don hallaka 'yan ta'adda da su ka addabi yankunan jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnati Za Ta Biya Diyyar Mutane 85 da Sojoji Su Ka Kashe da Bam a Kaduna

Atiku ya yi martani game da harin bam kan masu Maulidi

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi martani game da harin bam da aka kai kan masu Maulidi a jihar Kaduna.

Atiku ya kirayi Gwamnatin Tarayya da ta tsaurara bincike don gano dalilin faruwar hakan da kuma daukar mataki nan gaba.

Ya ba da shawarar kula da lafiyar wadanda su ka samu raunaka da kuma ba da taimako na musamman ga iyalan wadanda su ka mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel