Nijar: "Kada Ka Jefa Yankin Sahara Cikin Yaƙi" Sheikh Rijiyar Lemu Ga Tinubu

Nijar: "Kada Ka Jefa Yankin Sahara Cikin Yaƙi" Sheikh Rijiyar Lemu Ga Tinubu

  • Sheikh Muhammad Sani Rijiyar Lemu ya buƙaci shugaba Tinubu ya guje wa ɗaukar matakin soji kan gwamnatin sojin Nijar
  • Fitaccen Malamin na jihar Kano ya roki ECOWAS ta bi hanyar lalama wajen warware rikicin juyin mulkin
  • Wannan na zuwa ne yayin da shugaba Tinubu ya nemi amincewar majalisa na afka wa jamhuriyar Nihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano state - Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, ya bi sahun ‘yan Najeriya wajen roƙon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kar ya dauki matakin soji a kan gwamnatin Nijar.

Idan baku manta ba, ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) karƙashin Tinubu ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar wa'adin mako ɗaya su canja shawara.

Sheikh Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu.
Nijar: "Kada Ka Jefa Yankin Sahara Cikin Yaƙi" Sheikh Rijiyar Lemu Ga Tinubu Hoto: Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu
Asali: Facebook

ECOWAS ta umarci sojojin su maida wa hamɓararren shugaban ƙasa, Muhammed Bazoum mulki cikin mako ɗaya ko kuma ƙungiyar ta ɗauki matakin soji a kansu.

Kara karanta wannan

Fargabar Yaƙi: Jerin Jihohin Najeriya 7 da Suka Haɗa Boda da Jamhuriyar Nijar

Da yake tsokaci kan juyin mulkin a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Jumu'a, Malamin ya ce dangantar da ke tsakanin Najeriya da Nijar ta zarce maƙotaka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ya kamata Najeriya ta yi tunani a kan dangantakar da ke tsakaninta da ƙasar da kuma al'ummar jamhuriyar Nijar.

Sheikh Rijiyar Lemo ya ce ɗaukar matakin soji da yaƙi zai ƙara dagula lissafi ne, ya ƙara jefa al'umma cikin wahalhalu baya ga wahalhalun da suke fama da su.

Wace hanya ya kamata a bi wajen warware matsalar?

A kalamansa, Malamin ya ce:

"Ya kamata ECOWAS ta bi hanyoyin maslaha na zaman lafiya wajen warware wannan matsalar ga mutanen Nijar da yankin baki ɗaya, ba tare da jefa mutane cikin wahala ba."
"Kowa ya san abinda yaƙi ke kawo wa musamman a irin wannan lokacin, yana zuwa da abubuwa daban-daban, ba mu san lokacin da zai ƙare ba."

Kara karanta wannan

Jerin Matakai 7 Masu Tsauri da Shugaba Tinubu da ECOWAS Ke Shirin Ɗauka Kan Jamhuriyar Nijar

"Duniya ta canja kowace ƙasa burinta ta tara manyan makamai, kuma Nijar tana da makamashin Uranium, kuma ana ganin babu ƙasar da Allah ya bata wannan makamashi kamarta, abinda kasashen yamma ke nema kenan."

Sheikh Rijiyar Lemu ya ƙara da yin kira ga jagororin arewa su faɗa wa gwamnatin tarayya cewa ɗaukar matakin soja ba shi ne mafita daga halin da Nijar ta shiga ba.

“Ya kamata ‘yan majalisar mu, shugabanni da ‘yan jarida su wayar da kan al’umma game da matakin sojan da ake shirin dauka, su tabbatar da cewa bai yi nasara ba."

bidiyon malam a nan

Shugaba Tinubu Ya Aike da Sakon Shirinsa Na Tura Sojoji Nijar Ga Majalisar Dattawa

A wani labarin kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da majalisar tarayya shirin ƙungiyar ECOWAS na ɗaukar matakai kan jamhuriyar Nijar.

Hakan na kunshe a wata wasiƙa da ya tura zuwa majalisar kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙaranta a zaman yau Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel