Gwamnati za ta raba man fetur kyauta idan aka saba doka - DPR
- Ana ta faman rikici tsakanin Hukumar DPR da kuma ‘Yan kasuwar fetur IPMAN
- Masu jigilar man fetur sun ce ba za su saye mai a N190 sannan su saida a N145 ba
- ‘Yan kasuwa sun saye mai ne a N190 amma DPR ke takura masu su saida a N145
Mu na da labari cewa Gwamnati za ta raba man fetur kyauta a duk inda ake saida man ya haura farashin da Gwamnatin Tarayya ta kayyade. Hukumar DPR da ke lura da kayan mai a kasar ta bayyana hakan.
Hukumar ta DPR da ke Yankin Enugu tayi barazanar cewa za ta raba man fetur kyauta idan aka saba doka kamar yadda neman labarai su ka bayyana. Unyime Akpan wani babban Jami’in Hukumar na Yankin ya bayyana wannan a jiya Talata.
KU KARANTA: Naira ta samu tagomashi a kan Dalar Amurka
DPR ta rufe wasu gidajen mai a Jihar Anambra da ya saba wannan doka yayin da tace idan aka cigaba da saida litan man a farashin da yah aura N145 za su rabawa jama’a man fetur din ne kyauta. Hukumar tace duk wanda ba zai saida mai a haka ba ya hakura.
Sai dai masu harkar mai a kasuwa sun ce hakan ba shi zai kawo sauki ba. Shugaban masu jigilar mai a Yankin Enugu watau Ikechukwu Nwankwo yace idan ana neman kawo karshen wahalar man shi ne Hukumar NNPC ta saki fetur a ko ina a farashi mai rahusa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng