Ana ta kwan-gaba kwan baya kan wasikar IBB ga Buhari, shin waye yayi wasikar?
- SSS ta gayyaci mai magana da yawun bakin Janar Babangida
- An bukaci ya bayyana a hedkwatar tsaro a ranar Alhamis dinnan
- Femi Falana ya bukaci Sufeton 'yan sanda ya hakura da tuhumar Mista Afegbua
Majiyar mu Legit.ng ta rawaito mana cewar, Hukumar 'Yan sanda ta Farin kaya wato (SSS) ta gayyaci Kassim Afegbua, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Lauyan shi Kayode Ajulo, ya shaida wa majiyar mu cewar an gayyace shi ne ta hanyar kira a wayar tarho da hukumar 'yan sanda ta farin kaya suka yi mishi, inda aka bukaci ya bayyana a hedkwata kafin karfe sha daya na ranar Alhamis dinnan.
Gayyatar ta biyo bayan Mista Afegbua ya kai kanshi gurin hukumar tsaro a Abuja, bayan 'yan sanda sun bayyana shi a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo, saboda rubuta takarda da yayi a madadin tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida, wanda ya jagoranci kasar nan lokacin mulkin soja daga shekarar 1985 zuwa 1993.
DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tace kimanin mutane miliyan bakwai ke amfana da tsarin samar da aikin yi
Mista Afegbua ya sanya hannu akan takardar ranar Lahadin data gaba ta, inda tsohon shugaban kasar ya nuna shakku akan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, kuma ya bukaci da ya barwa matasa suma su dana a shekarar zabe mai zuwa ta 2019.
'Yan sanda sun bada sanarwar kamo Mista Afegbua a ranar Litinin dinnan da ta wuce, inda shi kuma ya kai kansa har hedkwatar hukumar tsaron, tare da lauyan shi a ranar larabar nan da safe. Bayan cinye kimanin minti 25 suna tattaunawa da kwamishinan 'yan sanda na yankin, sai gashi an saki Mista Afegbua ba tare da canjin shi komai ba.
A lokacin da lauyoyin sa suke ta shawara akan su daga kara saboda bata mishi suna da 'yan sanda suka yi, sai ga takarda daga hukumar tsaro ta farin kaya, inda suka bukaci ya bayyana a ranar Alhamis.
Babban lauyan nan Femi Falana, ya gargadi Babban Sufeton 'yan sanda, Ibrahim Idris, akan ya hakura da tuhumar Mista Afegbua, saboda hakan kamar keta mishi haddi ne.
Mista Afegbua yace tsohon shugaban kasar yana goyon bayan sa, kuma yayi alkawarin ganin ya kubuto dashi daga cikin matsalar da yake ciki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng