Yan Sanda Sun Sheke Yan Bindiga 50 a Yayin Wani Artabu

Yan Sanda Sun Sheke Yan Bindiga 50 a Yayin Wani Artabu

  • Ƴan bindiga masu yawa sun baƙunci lahira a wani artabu da suka yi da ƴan sanda, sojoji da ƴan sakai a Taraba
  • Jami'an ƴan sandan sun yi artabun da ƴan bindigan ne bayan sun samu bayanan shirinsu na kai farmaki wasu ƙauyuka
  • Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar ya fitar a birnin Jalingo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Rundunar ƴan sandan jihar Taraba a ranar Juma’a ta ce ta kashe ƴan bindiga sama da 50 a karamar hukumar Bali.

Kakakin rundunar Abdullahi Usman, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Jalingo babban birnin jihar, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP sun halaka yan sakai 2 a yayin wani farmaki

Yan sanda sun halaka yan bindiga a Taraba
Yan sanda sun halaka yan bindiga 50 a yayin wani artabu a Taraba Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Usman ya ce an kai harin ne a bayan samun bayanan sirri kan cewa wasu da dama da ake zargin ƴan bindiga ne sun mamaye ƙauyen Tonti kuma suna shirin yin garkuwa da jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sheƙe ƴan bindigan

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta samu labarin cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a cikin ɗaruruwan su (100) sun kai farmaki ƙauyen Tonti da ke ƙarƙashin gundumar Maihula da ke ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba."
"Ƴan bindigan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 5:30 na safe a daidai lokacin da musulmai ke gudanar da sallar Asuba, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi."
"Da samun bayanai, kwamishinan ƴan sandan jihar Taraba, Joseph Eribo ya ba da umarnin tura wata tawaga ta musamman daga reshen Bali zuwa yankin tare da haɗin gwiwar sojoji, ƴan sakai da mafarauta."

Kara karanta wannan

Jami'an yan sandan sun cafke gungun masu garkuwa da mutane a jihar Arewa

"Lokacin da suka isa ƙauyen, ƴan bindigan sun yi musayar wuta da tawagar haɗin gwiwar. A yayin artabun ƴan bindiga da yawa sun halaka, wasu sun samu raunuka yayin da sauran suke tsere."
"Bincike ya nuna cewa an kashe ƴan bindiga sama da 50 a artabun. A halin yanzu, ana cigaba da farautar ƴan bindigan a yankin da nufin kamo waɗanda suka tsere."

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya tura wata runduna ta musamman a yankin domin gudanar da sintiri mai ƙarfi da kuma daƙile kai hare-haren ƴan bindigan zuwa wani ƙauyukan da ke kewayen.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin yankin Bali mai suna Malam Muhammad wanda ya tabbatar da halaka ƴan bindigan.

Muhammad ya bayyana cewa tun da farko ƴan bindigan ne suka yi yunƙurin kawo farmaki, inda jami'an tsaron suka yi musu rubdugu.

Ƴan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan sanda sun samu nasarar cafke wasu gungun masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna.

Jami'an ƴan sandan sun samu nasarar cafke masu garkuwa da mutanen ne a wani sumame da suka kai a maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng