Yan Ta'addan ISWAP Sun Halaka Yan Sakai 2 a Yayin Wani Farmaki

Yan Ta'addan ISWAP Sun Halaka Yan Sakai 2 a Yayin Wani Farmaki

  • Ƴan ta'addan ISWAP sun halaka ƴan sakai mutum biyu a wani harin da suka kai a ƙauyen Katarko kusa da Gujba a jihar Yobe
  • Ƴan sakan dai sun rasa rayukansu ne a yayin da suke ƙoƙarin harin da ƴan ta'addan suka kai ƙauyen
  • Dakarun sojoji sun kawo ɗauki inda suka fatattaki ƴan ta'addan tare da halaka wasu daga cikinsu da ba a san ko na wa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - An halaka ƴan sakai mutum biyu a yayin da suke ƙoƙarin daƙile harin da aka kai a ƙauƴensu a jihar Yobe.

A cewar Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, an kai harin ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sheke yan bindiga 50 a yayin wani artabu

Mayakan ISWAP sun halaka yan sakai
Yan ta'addan ISWAP sun halaka yan sakai 2 a Yobe Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan ƙungiyar ta'addanci ta Da'esh (ISWAP) sun kai farmaki kan wani sansanin ƴan sakai a ƙauyen Katarko, kusa da Gujba a jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani majiyar soji ya bayyana cewa ƴan sakan sun yi artabu da ƴan ta’addan na tsawon mintuna 15 kafin daga bisani su samu goyon bayan dakarun runduna ta 27 Task Force Brigade.

Majiyar ta ce sojojin sun yi nasarar daƙile harin amma ƴan sakai biyu sun rasa rayukansu.

Ba a san adadin ƴan ta'addan da suka rasa rayukansu ba domin an ga ɓurɓushin jini wanda ya nuna cewa sun kwashe gawarwakin waɗanda suka rasu." A cewar majiyar.

A wata arangama makamanciyar haka, wasu mayaƙan na ISWAP sun kuma kai wa sojoji hari a wani shingen bincike tsakanin Jakana da Mainok a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Jami'an yan sandan sun cafke gungun masu garkuwa da mutane a jihar Arewa

An harbe biyu daga cikin ƴan ta'addan yayin da wasu suka tsere bayan sojoji sun buɗe musu wuta.

Zagazola Makama ya ce soja ɗaya ya samu rauni yayin fafatawar da aka yi da ƴan ta'addan.

Dakarun Sojoji Sun Halaka Mayakan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla sama da mutum 100 mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne suka halaka a wani hari da jiragen yaƙin rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai suka kai a jihar Borno.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a lokacin da ƴan ta'addan ke ganawa a dajin Bukar Mairam a ƙaramar hukumar Marte.

Asali: Legit.ng

Online view pixel