Siyasar Kano: Hadimin da Ganduje ya tsige, ya dawo yana neman kujerarsa a zaben 2023

Siyasar Kano: Hadimin da Ganduje ya tsige, ya dawo yana neman kujerarsa a zaben 2023

  • Takarar gwamna Kano ya dauki wani sabon salo, Salihu Tanko Yakasai zai nemi gwamna a 2023
  • Salihu Tanko Yakasai ya kudiri niyyan gaje kujerar tsohon mai gidansa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
  • Tsohon hadimin Gwamnan zai yi takarar gwamna ne a karkashin jam’iyyar hamayya ta PRP

Kano - A ranar Talata, 3 ga watan Mayu, 2022, Salihu Tanko Yakasai ya bada sanarwar zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Kano a zabe mai zuwa.

Malam Salihu Tanko Yakasai ya shaidawa Duniya wannan ne a shafinsa na Facebook dazu.

Yakasai ya fara jawabin ne yana mai jinjina da godiya ga Allah (SWT), ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023.

‘Dan siyasar ya tabbatar da cewa zai nemi kujerar gwamnan ne a jam’iyyar PRP da ya koma. Yakasai ya biya N2.5m ya yanki fam din shiga takarar.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Hakan ya na nufin Salihu Yakasai zai shiga zaben fitar da gwani da sauran masu neman mulki a PRP. Idan ya dace zai fuskanci APC, PDP da irinsu NNPP.

Addu’ar tsohon Darekta-Janar na harkokin yada labaran gidan gwamnatin Kano shi ne Ubangiji ya zabawa mutanen Kano mafi alheri, ko da waninsa ne.

Dawisu
Salihu Tanko Yakasai Hoto: Dawisu2016
Asali: Facebook

Jawabin Dawisun Kano

"Bismillahi tawakkaltu alallahi wala hawla wala quwwata illa billah. Da sunan Allah, Mai Rahama Mai jin kai, Mai kowa Mai komai, Mai bada mulki ga wanda Ya so, a sanda Ya so, Allah Mabuwayi!
Ina farin cikin sanar da yan'uwa da abokan arziki da sauran al'ummar jihar Kano, yanke shawarar tsayawa takarar Gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam'iyar PRP Nasara.
Da yardar Allah, zan yi taron baiyana takara ta ranar Juma'a mai zuwa, 6 ga watan May 2023, inda zan yi cikakken bayani na dalilai na.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Allah Ubangiji Ya zaba wa Kano mafi alheri, wannan itace adduar mu, ba lallai sai mu ba. Alhamdulilah
Salihu Tanko Yakasai
Dawisun Kano
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya."

Tarihin PRP a Kano

PRP ta na da tarihi a jihar Kano domin ta taba lashe zaben gwamna har sau biyu. Malam Aminu Kano shi ne ya kafa jam’iyyar a 1979, ya kuma rene ta.

A zaben 1979 Abubakar Rimi ya zama gwamna a karkashin PRP. Jam’iyyar ta hannun Sabo Bakin Zuwo ta samu nasara a 1983 bayan Rimi ya sauya-sheka.

Baya ga jihar Kano, jam’iyyar adawar ta kafa gwamnati a jihar Kaduna a lokacin Balarabe Musa.

Dawisu v Ganduje

Idan za a tuna, Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige Salihu Yakasai daga mukaminsa saboda ya soki gwamnatin Muhammadu Buhari.

A dalilin sukar Yakasai, jami’an DSS su ka tsare tsohon hadimin na kwanaki su ka yi masa tambayoyi. Bayan an fito da shi ya bada sanarwar barin APC.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

Asali: Legit.ng

Online view pixel