Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa

Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa

- An yi wa Aminu Ibrahim Daurawa tambaya game da zubar da maziyyi da azumi

- Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce wanda ya yi maziyyi zai rama azumi daya

- Wannan shi ne ra’ayin Malamai na Malikiyya irinsu Ibn Abi Zayd Al-Qayrawani

Wani Bawan Allah ya aiko wa Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa tambaya, inda ya nemi fatawa a kan zubar da maniyyi a lokacin da mutum yake azumi.

Wannan mutum ya bayyana cewa ya na cikin yin waya da budurwarsa a wayar salula, sai ya ji maniyyi ya fito daga gabansa, alhali azumi ya na bakinsa.

Kafin ya amsa tambayar, babban malamin na musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ja-kunne a kan yin waya irin wannan a lokacin da ake azumi.

KU KARANTA: Me ake nufi da niyya, kuma ya ake yin niyyar azumi - Pen Abdul

Shehin malamin ya ce ganganci ne mutum ya na dauke da azumi, kuma ya rika yin wayar da za ta iya motsa masa sha’awa a cikin watan azumi na Ramadan.

Aminu Ibrahim Daurawa ya nakalto fatawar babban malamin fikihu nan, Ibn Abi Zayd Al-Qayrawani, wanda ya ce irin azumin wannan Bawan Allah ya karye.

Sheikh Al-Qayrawani a littafinsa na Risala, ya ce wanda ya zubar da maziyyi da gangan a sanadiyyar sha’awa zai kama baki, sai ya rama azumi daya daga baya.

Haka zalika a fatawar bajimin malamin, duk wanda ya kai har ga zubar da maniyyi a lokacin azumi, sai ya yi kaffara; zai yi azumi 61 bayan watan na Ramadan.

Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa
Malam Aminu Daurawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Mabiyan Sheikh Abduljabbar su na so a bude masu masallacin saboda Ramadan

Wani Bawan Allah ne ya wallafa bidiyon wannan amsar tambaya a shafinsa na Twitter. Da alamu an yi karatun ne a garin Gombe inda malamin ya saba yin tafsiri.

A kwanan baya an yi wa wani malami irin wannan tambaya, inda ya ba mai neman wannan amsa shawarar ya fara da yin aure domin ya magance sha’awarsa.

A wani kaulin da ya sha ban-bam da fatawar malaman mazhabar malikiyya, fitar maziyyi ba ya karya azumi, amma an hadu a kan hakan zai nakasa ladar mutum.

A cikin irin wannan shirye-shirye na mu na goron Ramadan, kwanakin baya mun kawo maki jerin abubuwa 10 da ya kamata kowane Musulmi ya kiyaye da Azumi

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana game da abubuwan da ake bukatar mai azumi ya kiyaye. Daga ciki akwai karatun Kur'ani da kuma yawan yin salloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel