An Kama Tsohon Boka da Ya Zama Malamin Addini Kan Kisan Matarsa

An Kama Tsohon Boka da Ya Zama Malamin Addini Kan Kisan Matarsa

  • Jami'an yan sanda sun kama Fasto Abiodun Sunday kan zargin kashe matarsa, Tosin Oluwadare
  • An tattaro cewa mummunan al'amarin ya afku ne a Ido-Ile a karamar hukumar Ekiti ta Yamma a jihar Ekiti
  • Dan uwan marigayiyar, Samuel Ibironke, ya yi zargin cewa Fasto Abiodun ya makure yayarsa har lahira

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ido-Ile, jihar Ekiti - Jami'an rundunar yan sandan jihar Ekiti sun kama wani fasto, Abiodun Sunday kan zargin kisan matarsa, Tosin Oluwadare.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Sunday Abutu, ya ce mummunan al'amarin ya afku ne a yankin Ido-Ile da ke karamar hukumar Ekiti ta Yamma a jihar.

An kama fasto kan zargin kisan matarsa
An Kama Tsohon Boka da Ya Zama Malamin Addini Kan Kisan Matarsa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Abutu ya bayyana cewa rundunar na binciken lamarin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya buƙaci mataimakin gwamnan APC ya sa hannu a takardar murabus kan abu 1 tal

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa an kama wanda ake zargin ne tare da gawar a hanyarsa na fita daga garin.

An rahoto cewa an tura faston, wanda ya kasance tsohon boka, zuwa cocin Christ Apostolic a Ori-Oke, Ido Mountain, Ekiti ta Yamma, inda aka taba korar sa.

Wani dan uwan marigayiyar, Mista Samuel Ibironke, ya yi zargin cewa Fasto Abiodun ya makure yayarsa har lahira.

"Bayan ya kashe yayata, sai ya kira matata wacce take ma'aikaciyar asibiti kan ta zo ta taimaka masa, koda matata ta isa wajen sai ta gano cewa ya makure yayata ne har duniya."

Jaridar Leadership ta rahoto cewa mahaifiyar marigayiyar bata san wa ke kanta ba tun bayan mutuwar matar wacce ita kadai ce yar da ta haifa a duniya.

Basaraken garin ya yi martani

A nasa martanin, basaraken garin Olojudo na Ido-Ile, Oba Aderemi Obaleye, ya ce:

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa

“Wannan lamari ne mai matukar bakin ciki wanda ya kusa cinnawa garin wuta, saboda matasa sun yi zanga-zangar nuna adawa da abin da wanda ake kira da fasto ya aikata. Ina so hukumomi su binciki lamarin, su kuma gurfanar da wanda ya aikata laifin, domin ya zama izina ga saura."

Yan bindiga sun sace fasto da wasu 2

A wani labarin, mun ji cewa wasu mahara sun yi garkuwa da shahararren Fasto, Kingsley Eze a jihar Imo.

Maharan sun sace Kingsley ne da wani mutum daya a kauyen Umuekebi da ke karamar hukumar Isiala Mbano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel