Tinubu Ya Tura Sako Ga Majalisa Don Sake Karbo Bashin Dala Biliyan 8.69, Ya Fadi Dalilinsa

Tinubu Ya Tura Sako Ga Majalisa Don Sake Karbo Bashin Dala Biliyan 8.69, Ya Fadi Dalilinsa

  • Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisa don sake karbo bashin dala biliyan 8.69
  • Tinubu ya bukaci amincewar Majalisar ce don cika kudirin Gwamnati Tarayya na karbar bashin daga shekarar 2022 zuwa 2024
  • Shugaban ya bayyana cewa Bankin Duniya da na Raya Afirka sun yi alkawarin tallafawa bashin da naira biliyan 2.5

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa kan sake karbo bashin dala biliyan 8.69.

Har ila yau, Tinubu a cikin tsarin karbar bashin Gwamnatin Tarayya daga shekarar 2022 zuwa 2024 zai karbi Yuro miliyan 100.

Tinubu ya nemi amincewar Majalisa don ciwo bashin dala biliyan 8
Tinubu ya sake neman amincewar Majalisa don neman bashi. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yaushe Tinubu ya bukaci neman bashin?

Wannan na kunshe ne a cikin wata saanarwa da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a yau Talata 28 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Kwanaki 6 da dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu zai lula kasar Larabawa gobe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya ce Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka za su tallafa wa bashin da naira biliyan 2.5, cewar The Nation.

Shugaban ya ce wannan bashin da za a karbo an yi duba ne ganin yadda zai taimaka wa tattalin arziki da kuma ci gaban kasar baki daya.

Mene sanarwar ke cewa?

Sanarwar ta ce:

"Ina neman amincewar Majalisa kan karbo bashin da Gwamnatin Tarayya ta tsara karba daga shekarar 2022 zuwa 2024 don fara ayyuka.
"Kamar yadda Majalisar ta sani, gwamnatin Buhari ta amince da karbo bashin daga shekarar 2022 zuwa 2024 a ranar 15 ga watan Mayun 2023."

Tinubu ya kara da cewa wannan karbar bashin ya zama dole ganin yadda bangarori da dama na kasar ke cikin mawuyacin hali.

Ya bukaci Majalisar da ta yi gaggawar amincewa da ciyo bashin don bai wa gwamnati damar yi wa al'umma abin da ya dace, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Shettima ya fadi lokacin gyara tattalin arziki

A wani labarin, mataimakain shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana lokacin da tattalin arzikin Najeriya zai farfado.

Kashim ya ce nan da zuwa watanni 15 komai zai daidaita a kasar musamman bangaren tattalin arziki.

Mataimakin shugaban kasar ya ce Shugaba Tinubu ya himmati wurin tabbatar da inganta rayuwar al'ummar kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel