An Bankado Sabon Shirin Tayar da Hargitsi a Jihar Kano Kan Hukuncin Tsige Gwamna Abba

An Bankado Sabon Shirin Tayar da Hargitsi a Jihar Kano Kan Hukuncin Tsige Gwamna Abba

  • An nuna damuwa kan wata tarzoma da ake shirin tayarwa a garin Kano a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba
  • Kungiyar matasa ta PLYV ce ta ankarar da jama'a a wata sanarwa da ta saki a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba
  • A halin da ake ciki, an bukaci sufeto janar na yan sanda da rundunar DSS da su gaggauta shiga lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata kungiyar goyon bayan APC karkashin inuwar ‘Progressive League of Youth Voters (PLYV)’, ta nuna damuwa cewa gwamnatin jihar Kano na shirya zanga-zanga don tayar da tarzoma a babban birnin jihar a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, rahoton Blueprint.

Hakan ya biyo bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara na baya-bayan nan da ta tsige Gwamna Abba Yusuf daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

PDP ta kara shiga matsala yayin da kotun daukaka kara ta tsige yan majalisa 11 a jihar Filato

An nemi DSS ta ankara
Shari'ar gwamnan Kano: An ankarar da IGP, DSS kan wani shiri na tayar da tarzoma Hoto: Sayllou Diallo
Asali: Getty Images

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, a Abuja, Audu Usman Shuaibu, shugaban kungiyar na kasa ya bukaci hukumomin tsaro da su shiga lamarin sannan su kare mazauna Kano daga tashin hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shuaibu ya yi zargin cewa an shirya zanga-zangar ne don tsoratar da kwamitin Kotun Koli da ke jagorantar karar zaben gwamnan Kano da aka daukaka, ta yadda za a juya hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke nasara ya koma wajensu.

An nemi IGP da DSS su shiga lamarin

Sanarwar ta ce:

"Muna son ankarar da jama’a tare da yin kira ga Sufeto Janar na yan sanda da Darakta Janar na DSS kan ayyukan rashin imani da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf yake yi a kan kayen da ya sha na zabensa, a Kotun Daukaka Kara.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 2 muhimmai da ya kamata ku sani yayin da ake yanke hukuncin shari'ar zaben Nasarawa

"Tawagarmu a Kano ta sanar da mu cewa gwamnatin NNPP a jihar Kano ta kammala shiri tsaf don kwaso dubban masu tayar da tarzoma da sunan magoya bayanta daga kananan hukumomi 44 na jihar zuwa garin Kano don yin zanga-zanga a kan kayen da NNPP ta sha a Kotun Daukaka Kara.

Kungiya ta caccaki gwamnatin NNPP

Shuaibu ya nuna takaicinsa kan yadda gwamnati da aka daurawa alhakin kula da rayuka da dukiya za ta kitsa matakan da ka iya kai mutane ga halaka da asara.

Ya yi nuni ga abubuwan da gwamnatin ta yi a baya, yana mai misali da rusa kadarorin mutane da suka mallaka ta hanyar halal da gwamnatin ta yi wanda kudinsu ya kai sama da naira biliyan dari biyu cikin kwanaki shida da kama aiki.

Da yake kira ga hukumomin tsaro da abun ya shafa, Shuaibu ya roke su da su taimaka wajen kare rayukan mazauna garin Kano da al'ummar jihar Kano.

Kara karanta wannan

NNPP ta aika sako ga NJC kan hukuncin kotun daukaka kara na korar Gwamna Abba na Kano

Yayin da yake kira ga dattawa da shugabanni da su saita shugabannin NNPP, sanarwar ta ce:

"Wannan mataki na a mutu ko ayi rai yana da hatsari ga aman lafiya kuma ya zama dole a gaggauta yi wa tufkar hanci."

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan magoya NNPP sun gudanar da zanga-zanga a jihar ta arewa maso yamma.

A ranar Litinin ne gungun masu zanga-zangar suka mamaye wurare masu mahimmanci a cikin birnin wanda ya haifar da cunkoson ababen hawa da kuma cikas ga harkokin kasuwanci.

Daruruwan matasa da ke namawa Abba Yusuf adalci sun mamaye manyan tituna kamar su Kano-Zaria Road, Maiduguri Road da Kantin Kwari, rahoton Daily Trust.

Shari'ar Kano: An kama mutum 7

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa lamarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a jihar Kano na ci gaba da haifar da fargaba a jihar ta Arewa maso Yamma yayin da yan sanda suka bankado wani yunkuri na tayar da tarzoma a jihar.

Wannan ya kasance ne yayin da rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa ta bankado shirin da wasu kungiyoyi ke yi na haddasa tarzoma a jihar kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta tsige gwamnan, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel