Kotu Ta Fadi Ranar Hukuncin Shari'ar Dan China Kan Zargin Kisan Budurwarsa Ummita

Kotu Ta Fadi Ranar Hukuncin Shari'ar Dan China Kan Zargin Kisan Budurwarsa Ummita

  • Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar kisan kai da dan China, Geng Quarong ya yi a shekarar bara
  • Ana zargin Geng da kisan budurwarsa a Unguwar Janbullo da ke karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano
  • Kotun ta sanya ranar 6 ga watan Disamba don ci gaba da shari'ar kisan wanda ya sabawa dokar kasa sashe na 221

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar kotu a jihar Kano ta sanya ranar ci gaba da sauraran shari'ar dan kasar China, Frank Geng Quarong kan zargin kisan kai.

Ana zargin Quarong da kisan budurwarsa mai suna Ummulkusum Sani wacce aka fi sani da Ummita a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta bayyana ainahin wanda ya lashe zaben gwamnan Kebbi

Kotu za ta yi hukunci kan shari'ar dan China kan zargin kisan budurwarsa a Kano
Kotu za ta raba gardama a shari'ar dan China da marigayiya Ummita. Hoto: Haruna Kiyawa.
Asali: UGC

Yaushe kotun ta saka don yanke hukunci?

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari'a, Aminu Ado Maaji ta sanya 6 ga watan Disamba don ci gaba da sauraran shari'ar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin kotun, Baba Jibo ya ce an dakatar da shari’ar ce na tsawon watanni takwas saboda alkalin da ke kula shari’ar na cikin alkalan da ke jagorantar shari’ar kotunan zaben da aka gudanar.

A bara ne aka gurfanar da Geng a gaban kotun da ke kan hanyar Miller da zargin kisan kai wanda ya sabawa dokar kasa.

Geng ya amsa kisan Ummita da bakinsa

Da ake tuhumarshi, Geng ya shaidawa kotun cewa ya zo Najeriya ne a shekarar 2019 inda ya ke aiki da kamfanin Tufafi na BBY.

Wanda ake zargin ya kara da cewa ya kashe wa marigayiyar sama da naira miliyan 60 yayin da su ke cin moriyar soyayyarsu.

Kara karanta wannan

Yanzu: Kotun Daukaka Kara ta kori kakakin majalisar Bauchi

TheCable ta tattaro cewa an sanar da kisan Ummita ne a ranar 17 ga watan Satumbar bara a Unguwan Janbullo.

An kama dan China da zargin kisan kai

A wani labarin, rundunar 'yan sanda ta cafke Geng Quarong da zargin kisan kai a Kano.

Ana zargin dan China, Geng da kisan budurwarsa mai suna Ummulkulsum wacce aka fi sani da Ummita.

Geng ya bayyana cewa ya kashe wa marigayiyar fiye da naira miliyan 60 lokacin da su ke soyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.