‘Wuka Na Caka Mata:’ Dan China Ya Amsa Laifinsa Na Kashe Budurwarsa ’Yar Kano, Ummita

‘Wuka Na Caka Mata:’ Dan China Ya Amsa Laifinsa Na Kashe Budurwarsa ’Yar Kano, Ummita

  • Dan kasar China da ya kasha Bahaushiya ‘yar jihar Kano ya amsa laifinsa, ya ce da kansa ya caka mata wuka ta mutu
  • Ya bayyana adadin kudaden da ya kasha mata a lokacin da suke soyayya amma kuma ta yaudare shi ta ki aurensa
  • An ruwaito a baya yadda aka kai ruwa rana kan yadda dan China ya yi barna, ya shiga har gida ya kasha budurwarsa

Jihar Kano - Frank Geng Quarong, Bacanisen da ake zargin ya hallaka budurwarsa a jihar Kano; Ummukulsum Sani Buhari ya amsa soke budurwar tasa da wuka, ya sheke ta da kansa.

Frank Geng Quarong ya bayyana hakan ne a gaban Babbar Kotun Kano a zaman da ake na ci gaba da sauraran shari’ar kisan a yau Laraba 29 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

"Biyayya Na Ke Wa Mijina", Matar Da Aka Kama Da Ƙanwarta Da Ganyen Wiwi a Jihar Katsina

Da lauyar gwamnatin Kano, Barisha Aisha Muhammad ta tambaye shi game da kisan, Geng ya amsa a gaban kotu cewa, shi ya aikata mummunan aikin.

Dan China ya amsa kisan Bahaushiya 'yar Kano
Ummita da Geng dan China | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wacce sana’a Geng ke yi a jihar Kano?

Hakazalika, ya ba da bahasin cewa, ya shigo Najeriya ne a 2019, inda ya kama aiki a kamfanin atamfa da yadi na BBY Textile, inda yake kwashe N1.5m a matsayin albashi duk wata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa, baya ga aikinsa, yana gudanar da harkokinsa na kasuwanci a Najeriya don samun na abin ka.

‘Yan kasashen waje kan shigo Najeriya domin yin ayyukansu, wasu sukan shigo bisa ka’ida wasu kuma ta barauniyar hanya.

A rahoton da Aminiya ta fitar, an ce Geng ya ce ya kasha kudade masu yawa kan Ummita, kusan miliyan 60 a lokacin da tsuntsuwar soyayyarsu ke kada fiffike.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

Ni da kaina na kashe Ummita da wuka, inji Geng

A kalamansa a gaban kotu, ya ce da kansa ya dauki wuka ya caka wa Ummita, lamarin da ya kai ga mutuwarta ba tare da shurawa ba.

A bangaren lauyan Geng, Barista Muhammad Balarabe Dan-Azumi ya ce akwai shaida daya ta karshe da zai gabatar.

Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya dage ci gaba da sauraran karar zuwa ranar Alhamis 30 ga watan Maris don ganin yadda za ta kaya.

A baya rahoto ya bayyana Geng ya musanta kasha Ummita a gaban kotu, amma a yanzu ya amsa tare da bayyana gaskiyar yadda lamarin ya faru. Daga baya kuma, ya ce shi kansa bai son a kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.