'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Kakakin Majalisa, Ana Zargin Jami'an Tsaro da Hannu a Harin

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Kakakin Majalisa, Ana Zargin Jami'an Tsaro da Hannu a Harin

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan kakakin Majalisar jihar Ribas, Edison Ehie a birnin Port Harcourt da ke jihar
  • Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 19 ga watan Nuwamba a gidan kakakin Majalisar da ke Port Harcourt
  • Ana zargin harin na da alaka da kokarin ajalin kakakin Majalisar wanda ya ke goyon bayan Gwamna Fubara

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ribas - Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari gidan kakakin Majalisar jihar Ribas, Edison Ehie.

Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 19 ga watan Nuwamba a gidansa da ke Port Harcourt babban birnin jihar, cewar The Nation.

'Yan bindiga sun kai hari gidan kakakin Majalisar jihar Ribas
Ana zargin jami'an tsaro da hannu a cikin hari. Hoto: Simi Fubara.
Asali: Facebook

Yaushe aka kai harin jihar Ribas?

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota a Kano ya yi sanadin salwantar rayuka 4 da jikkata wasu da dama

Idan ba a mantaba, Majalisar jihar ta tsige Edison daga mukaminsa a Majalisar kafin daga bisani ya ayyana kansa a matsayin kakakin Majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne yayin da Majalisar ta yi yunkurin tsige Gwamna Simi Fubara na jihar Ribas a kwanakin baya.

Wata majiya ta tabbatar da cewa har yanzu babu cikakken bayani kan harin duk da cewa jami'an tsaron Ehie sun dakile harin, cewar Channels TV.

Su wa ake zargi da kai wannan hari a Ribas?

Wani shaidan gani da ido da aka bayyana da Ken ya ce wannan wani yunkuri ne na kisan kai kan kakakin Majalisar.

Ya ce idan wani abu ya faru da Ehie to manyan jami'an tsaron jihar na da hannu a cikin harin saboda zargin wani babban jami'in tsaro da ya jagoranci kai harin.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan Shehu Shagari tsohon shugaban kasar Najeriya

Ya ce:

"A jiya Lahadi 19 ga watan Nuwamba da misalin karfe 11 na dare, wasu 'yan bindiga da jami'an tsaro sun kai hari gidan kakakin Majalisar jihar, Barista Edison Ehie.
"Har ila yau, jami'an tsaron kakakin Majalisar sun dakile harin a wani artabu da su ka yi da 'yan bindigan da jami'an tsaro.
"Ya na da muhimmanci ku sani cewa na'urar CCTV ta nadi komai dangane da harin wanda daga bisani za a sake su gidan talabijin na kasar da ma na kasashen waje."

Majalisa ta yi yunkurin tsige Gwamna Simi na Ribas

A wani labarin, Mambobin Majalisar jihar Ribas sun yi yunkurin tsige Gwamna Simi Fubara daga kujerarshi ta gwamna.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun sabani tsakanin gwamnan da mai gidansa Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.