Mummunan Hatsarin Mota a Kano Ya Yi Sanadin Salwantar Rayuka 4 da Jikkata Wasu da Dama

Mummunan Hatsarin Mota a Kano Ya Yi Sanadin Salwantar Rayuka 4 da Jikkata Wasu da Dama

  • Mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane hudu tare da jikkata wasu da dama a karamar hukumar Takai da ke jihar Kano
  • Lamarin ya faru ne a kauyen Dinyar Madiga da ke karamar hukumar a ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba
  • Kakakin hukumar kashe gobara a jihar, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi 19 ga watan Nuwamba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Akalla mutane hudu ne su ka mutu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne da yammacin Juma’a 17 ga watan Nuwamba a kauyen Dinyar Madiga da ke karamar hukumar Takai da ke jihar.

Akalla mutane hudu ne su ka rasa rayukansu a wani hatsarin mota a jihar Kano
Hatsarin mota a Kano ya yi sanadin salwantar rayuka da dama. Hoto: FRSC.
Asali: Facebook

Mutane nawa su ka mutu yayin hatsarin?

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan Shehu Shagari tsohon shugaban kasar Najeriya

Rahotanni sun tabbatar cewa mutane da dama sun samu munanan raunuka yayin hatsarin motar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin hukumar kashe gobara a jihar, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi 19 ga watan Nuwamba.

Ya bayyana cewa hatsarin ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane hudu da kuma raunata wasu da dama.

Ya ce:

“An kawo rahoton cewa wasu mutane uku akan babur sun yi kokarin wuce motar bas wanda hakan ya yi sanadin hatsarin da konewar motar kurmus.”

Mene hukumar kashe gobara ke cewa?

Ya ce bayan isowar jami’ansu sun samu mutane hudu ba sa cikin hayyacinsu inda su ka yi kokarin farfado da mutane shida tare da direban bas din.

Abdullahi ya kara da cewa an garzaya da su asibitin NYSC da ke Takai don ci gaba da ba su kulawar gaggawa, Mail News ta tattaro.

Kara karanta wannan

A kan hanyarsu ta neman mafita bayan shan kaye a zabe, 'yan jami'yya su 10 sun mutu a hatsarin mota

A cewarsa:

“Abin takaici likitoci sun tabbatar da mutuwar mutane hudu wanda ba a iya gane ko su wane ne ba.
“Binciken da aka gudanar ya nuna cewa hatsarin ya afku ne sakamakon tukin ganganci na wani mai babur da ya yi kokarin wuce motar bas.”

Kakakin hukumar FRSC a jihar, Labaran Abdullahi ya bayyana cewa sun samu labarin hatsarin inda ya ce za su yi bincike daga ofishinsu.

‘Yan jam’iyyar SDP 10 sun mutu a hatsarin mota

Kun ji cewa, akalla mutane 10 su ka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Kogi.

Hatsarin ya afku ne a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba inda ya rutsa da wasu ‘yan jam’iyyar SDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.