“Abin Duniya Ke Rudar ’Yan Najeriya”, Buhari Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Zabukan Shugaban Kasa

“Abin Duniya Ke Rudar ’Yan Najeriya”, Buhari Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Zabukan Shugaban Kasa

  • Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasar Najeriya ya ba da labarin yadda ya sha gwagwarmaya a zaben 2003, 2007 da 2011 da ya sha kaye
  • Buhari ya ce duk da Najeriya kasa ce wacce ba ta kai matakin kasashen da suka ci gaba ba, amma 'yan kasar na son rayuwar fantamawa da son abin duniya
  • Ya ce burin 'yan kasar bai wuce mallakar gida mai girma da tsada ba, motocin fantamawa na alfarma, zuwa kasashen waje akai-akai da sauran su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daura, jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun fi ruduwa da abin duniya.

Ya yi ikirarin cewa hakan ya sa ya samu kalubale wajen samun nasara kan manyan mutane da yawa a yakin neman zaben shugaban kasa da bai yi nasara ba a 2003, 2007 da 2011.

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Khalil ya fadi abin da zai faru a Kotun Koli, ya bai wa Kwankwaso, Abba Kabir shawara

Muhammadu Buhari
Buhari ya ce burin 'yan Najeriya mallakar gida mai girma da tsada, motocin fantamawa na alfarma, zuwa kasashen waje akai-akai
Asali: Twitter

Yan Najeriya na da son abin duniya, cewar Buhari

“Nijeriya, ku yarda ko kar ku yarda, mu kasa ce da ba ta kai matakin kasar da ta ci gaba ba. Abubuwan kyale-kyale na matukar burge mu sosai."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wani lokacin kuma ba mu damu da ina za mu samun kudi ba, mu dai mu yi arziki kawai. Mu mallaki gida mai girma da tsada, motocin fantamawa na alfarma, zuwa kasashen waje akai-akai".

A cewar Buhari a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Najeriya NTA da yammacin ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.

Da yake tuna baya game da takarar shugaban kasa guda uku da ya yi amma bai yi nasara ba, ya ce:

"Na sami kaina ina gwagwarmaya don neman goyon bayan manyan mutane, amma na fahimci abin duniya ya fi rudar 'yan Najeriya maimakon yin abubuwan da za su taimaki marasa galihu."

Kara karanta wannan

Cikakken bidiyon hirar Buhari ta farko bayan barin fadar shugaban kasa ya bayyana

Buhari ya ce mulkin Najeriya akwai wahala

A wani labarin, tsohon shugaban kasar ya koka da cewa ‘yan Najeriya su na da wahalar jagoranta saboda su na ganin sun fi mai mulki sanin abin da ya dace, Legit Hausa ta ruwaito.

Jaridar The Cable ta ruwaito Buhari na cewa idan ya ba mutum mukami, ya na kyale shi ya yi aikinsa, ya ce wannan ne rauninsa.

Mai girma Buhari ya nuna babu mamaki an samu wasu miyagu da su ka juya madafan iko a lokacinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel