Cikakken Bidiyon Hirar Buhari Ta Farko Bayan Barin Fadar Shugaban Kasa Ya Bayyana

Cikakken Bidiyon Hirar Buhari Ta Farko Bayan Barin Fadar Shugaban Kasa Ya Bayyana

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi dogon jawabi a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Najeriya NTA
  • A yayin hirar, Buhari ya bayyana cewa bai yi kewar lokacin da ya ke shugaban kasa ba, kuma da aka tambaye shi game da lafiyarsa
  • Duk da cewa yana zaune a Daura, jihar Katsina, mai nisa da babban birnin kasar, Buhari ya bayyana cewa har yanzu mutane suna ziyartarsa ​​akai-akai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daura, jihar Katsina - A karon farko tun bayan mika wa shugaban kasa Bola Tinubu mulki a watan Mayu, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi dogon jawabi a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Najeriya NTA.

Kara karanta wannan

Yadda muka sha kaye a zaben 1998 domin na ki bai wa INEC cin hanci, Obasanjo

NTA ta fitar da hirar ne ta musamman a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, inda daga nan ne mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya raba bidiyon a shafin X.

Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban kasa Buhari ya yi magana game da gwamnatin sa a wata hira ta musamman ta NTA. Hoto: @GarShehu, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Kalli bidiyon a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari yayi magana akan gwamnatin sa da lafiyar sa

Tsohon shugaban kasar, ya nanata cewa ya yi bakin kokarinsa a shekaru takwas da ya yi a ofis, ya na mai cewa bai san ko ya iya cin ma nasara ba.

Da aka tambaye shi ko kwalliya ta biya kudin sabulu ganin ya yi takara har sau hudu, Buhari ya nuna lamarin ba yadda dai aka so ba.

Ya ce an samu saukin ta’addancin Boko Haram lokacin da ya sauka, a halin yanzu ya na mahaifarsa a Daura, Legit ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya su na da wuyar sha'ani' Buhari ya bayyana abu 1 da jawo matsala a gwamnatinsa

Buhari ya ce mulkin Najeriya akwai wahala

Tsohon shugaban ya koka da cewa ‘yan Najeriya su na da wahalar jagoranta saboda su na ganin sun fi mai mulki sanin abin da ya dace.

Duk da yadda ta kasance a mulkinsa, Buhari ya ce idan ya ba mutum mukami, ya na kyale shi ya yi aikinsa, ya ce wannan ne rauninsa, The Cable ta ruwaito.

Mai girma Buhari ya nuna babu mamaki an samu wasu miyagu da su ka juya madafan iko a lokacinsa.

Buhari ya magantu kan canja fasalin kudin Najeriya

Buhari yake cewa ya amince a canza kudi daf da zai bar mulki ne saboda ya kare mutuncinsa kuma ya nuna arziki sai an yi gumi.

Ko a yau zai samu wata damar, Muhammadu Buhari yake cewa yadda ya yi mulki tsakanin 2015 da 2023, hakan dai zai sake maimaitawa.

“Da Na Koma Jamhuriyar Nijar”, Buhari

Kara karanta wannan

Buhari ya ambaci babban rauni 1 da yake da shi wanda ya iya kawo cikas a mulkinsa

Duk da komawa zama da ya yi a nesa da babban birnin tarayyar kasar, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa mutane na daukar motoci don kai masa ziyara a Daura.

Buhari ya ce:

"Mutane na hayar motocin bas suna zuwa ganina lokaci zuwa lokaci. Na zata na yi nesa da Abuja amma duk da haka suna zuwa. Da na lula Nijar da ace boda a bude yake."

Asali: Legit.ng

Online view pixel