Ruguntsumi Yayin da NLC Ta Garkame Mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, Ta Yi Abu Daya

Ruguntsumi Yayin da NLC Ta Garkame Mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, Ta Yi Abu Daya

  • Kungiyar Kwadago ta NLC, ta garkame ma’aikata da kuma mambobin Majalisar Tarayya a harabarsu da ke Abuja
  • Kungiyar NLC ta umarci dukkan ma’aikata su shiga yajin aiki a yau Talata saboda cin zarafin shugabanta, Joe Ajaero a Imo
  • Daga bisani mambobin kungiyar sun bude wa ‘yan jaridu kofa inda suka samu zarafin fita daga cikin Majalisar

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An garkame Majalisar Tarayya da ke Abuja a yau Talata 14 ga watan Nuwamba saboda yajin aiki, cewar TheCable.

Kungiyar NLC ta umarci dukkan ma’aikata su shiga yajin aiki a yau Talata 14 ga watan Nuwamba saboda cin zarafin shugabanta, Joe Ajaero a jihar Imo.

Kara karanta wannan

Ba haka muka yi namu ba, Oshimole ya yi martani kan tsarin NLC, ya ba ta shawara

Kungiyar NLC ta rufe Majalisar Tarayya kan kin bin umarninta na yajin aiki
NLC Ta Garkame Mambobin Majalisar Tarayya a Abuja. Hoto: NLC.
Asali: Twitter

Wane mataki NLC ta dauka a Majalisar?

Har ila yau, an takaita zirga-zirgan mutane da ababan hawa a kusa da harabar Majalisar, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kulle dukkan mambobin Majalisar na Tarayya guda biyu da ma’aikatansu da ‘yan jaridu yayin da mashigar ta ke garkame.

Bayan kai ruwa rana, daga bisani mambobin kungiyar sun bude wata mashiga yayin da wasu ‘yan jaridu suka samu fice wa, cewar Daily Post.

Wane martani jama'a suka yi kan matakin NLC?

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu kan wannan matakin NLC:

Zainab Muhammad ta ce abin da kawai ake bukata shi ne walwalar jama'a ba irin wannan lamari da zai kawo cikas ga zaman lafiya ba.

Aliyu Kabir ya ce:

"Shi bai san ma ana yajin aiki ba a kasar kawai ji ya yi ana fada, amma matakin da suka dauka bai kamata ba."

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

Khalid Muhammad ya ce hakan ya yi daidai tun da suma Majalisar 'yan kasa ne dole su shiga yajin aiki.

Oshiomole ya soki tsarin kungiyar NLC

A wani labarin, tsohon shugaban kungiyar NLC, Adams Oshiomole ya caccaki tsarin da kungiyar NLC ke yi a yanzu yayin yajin aiki.

Oshiomole wanda ya shugabanci kungiyar daga 1999 zuwa 2007 ya ce kungiyar ta mayar da kanta ta siyasa a fili.

Ya ce ma'aikata na cikin matsaloli a Najeriya kamata ya yi ta nemo hanyar magance matsalolin cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel