Wata Mata da Ta Auri Miji Dan Tsurut ta Baje Kolin Cikinta, Ta Haifo Santaleliyar Jaririya

Wata Mata da Ta Auri Miji Dan Tsurut ta Baje Kolin Cikinta, Ta Haifo Santaleliyar Jaririya

  • Wata mata da ta aurin wada ta saki hotunanta dauke da juna biyu, da wanda ke nuna lokacin da ta haihu
  • Matar, Kahboh Patience Fokong da mijinta, Derrick, sun samu arzikin haihuwar diya mace
  • Sun wallafa hotunan a shafinsu na Facebook don sanar da mabiyansu wannan labari mai dadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wata mata ta baje kolin juna biyu da take dauke da shi sannan ta sanar da cewar ita da mijinta sun samu 'karuwa.

Kahboh Patience Fokong ta ce Allah ya azurta ta da mijinta da haihuwar diya macve.

Mata da mijinta dan tsurut sun samu karuwa
Wata Mata da Ta Auri Miji Dan Tsurut ta Baje Kolin Cikinta, Ta Haifo Santalelen Jinjiri Hoto: Patience & Derick-DK Show.
Asali: Facebook

Patience ta garzaya dandalin Facebook domin wallafa hotunanta a lokacin da take dauke da juna biyu, tana mai baje kolin yadda cikin ya amsheta.

A cikin hotunan, an gano ta tare da mijinta, Derrick, wanda ya kwantar da kanta a kan cikin nata.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Abuja yayin da tayar jirgi ta cije yana tsaka da tafiya bayan sauka a tasha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'auratan sun shiga daga ciki a farkon shekarar 2023, kuma Patience ta sanar da Legit cewa ta fuskanci kalubale da dama kafin auren.

Ta ce wasu daga cikin kawayenta basu goyi bayan ta auri mutum mai kankanta kamar mijinta ba, amma ta ce ta ji ta gani.

Ta ce:

"Kwarai na fuskanci kalubale da dama lokacin da mijina ya nuna aniyarsa na aurena. Na fada ma iyayena, kuma duk basu yarda ba illa mahaifiyata, wacce ta kasance tare da ni sannan ta bukaci da na bi zuciyata. Kawayena suna ta yi mani ba'a, suna ta jikana da maganganu iri-iri haka wasu daga cikin dangi na."

Da zuwan diyarsu, Patience ta mika nasarar da ta samu wajen haihuwa ga Allah. Ta rubuta a Facebook:

"A karshen karshe, Allah ya yi mun da karfi. Ku tayamu yi wa lafiyayyiyar diyarmu maraba da zuwa cikin iyalinmu."

Kara karanta wannan

Wata mata ta yada bidiyon wani halitta da ta gani a dakinta, bidiyon ya girgiza intanet

Jama'a sun taya Patience da mijinta murna

Nkubi ya ce:

Ina taya Patience da Derick murna mai tarin yawa. Allah ya albarkaci karamar gimbiyar cikin koshin lafiya ya raya ta."

Waah Bae ta ce:

"Allah ya rubanya ni'imar da ya yi maku. Sannu da zuwa yar diya."

Wata mata ta haihuwa a mota

A wani labarin, mun ji cewa wata mata mai juna biyu ta haifi wata jariri a cikin motar kasuwanci da ta nufi garin Warri a jihar Delta.

Mai amfani da TikTok, @estacyc, ta sanya bidiyo kan yadda matar ta haihuwa a TikTok, inda ta yi nuni da cewa da mahaifiyar da abin da ta haifa duk suna raye cikin ƙoshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel