Bashin N500bn Da Ganduje Ya Bari Ne Ya Hana Mu Fara Aiki Kan Lokaci, Gwamnatin Kano

Bashin N500bn Da Ganduje Ya Bari Ne Ya Hana Mu Fara Aiki Kan Lokaci, Gwamnatin Kano

  • Gwamnatin NNPP ta ce Ganduje ya tafi ya bar dumbin bashi da ya haura naira biliyan 500, sabanin naira biliyan 300 da ta gano da farko
  • A cewar NNPP, wannan bashin da Ganduje ya ciyo, ya kawo cikas ga gwamnatinsu ta NNPP wajen gudanar da ayyuka a jihar Kano
  • Duk da hakan, jam'iyyar ta jinjinawa Abba Kabir na irin ayyukan da yake shimfidawa a jihar daga dan abun da jihar ke samu a yanzu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Gwamnatin jam'iyyar NNPP mai ci a jihar Kano ta zargi gwamnatin da ta shude ta jam'iyyar APC, karkashin Abdullahi Umar Ganduje da barin bashin sama da naira biliyan 500.

Kara karanta wannan

‘'Gwamnatin Tinubu za ta tsamo 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci,’' Betta Edu

Mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana hakan a Kaduna yayin jagorantar taron jam'iyyar NNPP na shiyyar Arewa maso Yamma.

Abba Kabir da Abdullahi Ganduje
A cewar NNPP, babu abin da Gwamna Abba ya samu da ya hau mulkin Kano Hoto: Abba Kabir da Abdullahi Ganduje
Asali: Facebook

Ya ce bashin da gwamnatin da ta shude ta bari a jihar Kano ya haura naira biliyan 500, kamar yadda binciken da suke yi yanzu ya nuna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamnan ya kuma ce wannan bashin ya kawo cikas ga gwamnatinsu ta NNPP wajen gudanar da ayyuka a jihar Kano, kamar yadda jaridar Premium ta ruwaito.

A yayin da ya ke zayyana irin nasarorin da gwamnatinsu ta samu a cikin kankanin lokaci, Abdussalam, ya kuma tabbatar wa shuwagabannin jam'iyyar cewa, gwamnatin NNPP mai ci ba za ta bai wa al'ummar Kano kunya ba.

Gwamnatin Abba za ta biya kudaden fansho da garatuti - Abdussalam

Abdussalam ya ce:

"A lokacin da muka karbi mulki, gwamnatin da ta shude ba ta bar mana komai ba sai dumbin bashi. Da farko bashin naira biliyan 300 ne, amma da muka ci gaba da bincike, yanzu mun gano naira biliyan 500, a hakan ba a gama bincike ba."

Kara karanta wannan

Cin zarafi: Kungiyar NLC ta fadi ranar tsunduma yajin aiki, ta tura bukatu 6 ga gwamnati

"Da zaran mun kammala binciken, za mu sanar da 'yan Nigeria, musamman al'ummar Kano irin dumbin bashin da gamnatin da ta shude ta tafi ta bari."

Ya kuma tariyo irin namijin kokarin da gwamnatin jihar ke yi karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na yin amfani da abubuwan da take da su a kasa wajen yi wa jihar Kano aiki.

"Gwamnatin Abba na biyan ma'aikata albashinsu ba tare da gibi ba, haka zalika ta biya duk wani bashi da ma'aikata ke bi. Haka zalika, daga wannan watan za a fara biyan duk wani mai bin jihar kudin fansho da giratuti, musamman ga iyalan ma'aikatan da suka riga mu gidan gaskiya."
"Akan wannan yunkuri, gwamnati ta ware naira biliyan shida domin biyan hakkokin ma'aikatan, ta hanyar farawa da 'yan mataki na daya zuwa na shida, kasancewa su ne kananun ma'aikata wadanda suka fi shan wahala."

A cewar Abdussalam, wanda kuma ya tabbatar da cewa tuni aka fara shirye shiryen tantance wadanda za su amfana a karshen watan nan.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun yi fatali da tsagin Atiku, sun koma goyon bayan shugaba Tinubu kan abu 1 tak

Ba Zan Biya Duk Wani Bashi Da Ganduje Ya Ciyo Wa Kano Ba - Abba Gida-Gida

Idan ba a manta ba, bayan kammala zaben gwamnan jihar Kano na shekarar 2023 da kuma ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, Abba, ya bayyana cewa ba zai biya duk wani bashi da Ganduje zai ciyo wa Kano bayan zaben ba.

Legit Hausa ta ruwaito wata sanarwa da sakataren yada labaran zababben gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar , ya ce, daga ranar 18 ga watan Maris zuwa 29 ga watan Mayu, kada wani mai bayar da bashi (gida da waje) ya sahale ko ya bayar da bashi ga gwamnatin Kano ba tare da ya tuntubi gwamnati mai jiran gado ba .

Asali: Legit.ng

Online view pixel