Ministan Tsaro da Hafsun Soja Sun Tafi Kasar Waje Domin Shigo da Wasu Jiragen Yaki

Ministan Tsaro da Hafsun Soja Sun Tafi Kasar Waje Domin Shigo da Wasu Jiragen Yaki

  • Ministan harkokin tsaro da shugaban hafsun sojojin saman Najeriya sun kai ziyara zuwa kasar Turkiyya a halin yanzu
  • Makasudin ziyarar ita ce a shigo da wasu jiragen yaki da za su taimaka wajen ganin bayan migun ‘yan bindiga a kasar nan
  • Muhammad Abubakar Badaru ya yaba da irin cigaban da Turkiyya ta samu, ya nemi hadin-kai tsakanin kasar da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya yi shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ministan harkokin tsaro, Muhammad Abubakar Badaru da shugaban hafsun sojojin sama, Hassan Abubakar sun tafi ketare.

Bayanin da aka fitar a shafin runduna sojojin sama sun tabbatar da cewa ana so a gaggauta shigo da jiragen saman T-129 ATAK.

Gwamnatin Najeriya ta biya kudin jirage shida na T-129 ATAK, nan da makonni biyu ake sa ran jiragen za su shiga hannun sojin sama.

Kara karanta wannan

Ya kamata CBN ta sa a daina amfani sabbin takardun Naira da Buhari ya kawo, malami ya fadi dalilai

Jiragen yaki
Jiragen yaki: Ministan tsaro a Turkiyya Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a kawowa Najeriya jiragen yaki

Sanarwar ta ce daga yanzu zuwa tsakiyar shekarar 2024, za a kawo ragowar jirage hudun, hakan zai bada damar tunkarar 'yan bindiga.

A matsayinsa na Darektan yada labarai na NAF, Air commodore Edward Gabkwet ya sanar da haka a shafin Facebook a ranar Lahadin nan.

Air commodore Edward Gabkwet ya ce Ministan tsaron Najeriyan ya zauna da takwaransa na kasar Turkiyya watau Mr. Yasar Guler.

Najeriya za ta hada-kai da Sojojin Turkiyya

Shi kuwa Guler ya yi alkawarin sojojin Turkiyya za su taimakawa Najeriya ta fuskar tsaro da soji wajen ganin an kawar da masafin ta’addanci.

Ministan Najeriyan da na kasar wajen sun ziyarci kamfanonin Turkiyya irinsu Turkish Aerospace Industries, MKE, Aselsan da Roketsan.

Da yake jawabi, Badaru Abubakar ya ce Turkiyya ta na cikin kasashen da su ka yi zarra a bangaren tsaro da fasahar kayan yaki a duk duniya.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah Ya Yi Wa Ohinoyi na Kasar Ebira Ado Ibrahim Rasuwa a Asibitin Abuja

Ministan ya dauki alwashin kawo karshen rashin tsaro bayan rantsar da shi.

Aikin sabon Ministan Abuja

A bangare guda, ana da labari sabon ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike, ya dage wajen ganin yadda za a tara makudan kudin shiga.

Dabbaka dokar haraji za ta kai mutane kurkuku ko akalla a ci su tarar dukiya bayan Gwamnatin Bola Tinubu ta baWike kujera mai tsoka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel