Da dumi-dumi: A karshe NAF ta magantu kan harin ta’addanci a sansanin Kaduna

Da dumi-dumi: A karshe NAF ta magantu kan harin ta’addanci a sansanin Kaduna

  • An bayyana rahoton da ke cewa ‘yan ta’adda sun kaiwa wani sansanin sojan saman Najeriya hari a Kaduna a matsayin na bogi
  • Kakakin NAF din Air Commodore Edward Gabkwet ya bayyana cewa babu wani hari da aka kai wurin a ranar Asabar, 26 ga watan Yuni
  • Gabkwet a cikin wata sanarwa ya bukaci jama'a da su yi watsi da labarin saboda gaba daya karya ne

An yi watsi da wani rahoto da ke ikirarin cewa ‘yan ta’adda sun kai wa sansanin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) da ke Kaduna hari a ranar Asabar, 26 ga watan Yuni.

Legit.ng ta tattaro cewa mai magana da yawun NAF, Air Commodore Edward Gabkwet ne yayi wannan bayani a wani sako da aka wallafa a shafin rundunar.

KU KARANTA KUMA: Tubabben dan IPOB ya jagoranci ‘yan sanda wajen kashe ‘yan ta’adda da lalata sansanoninsu a Imo

Da dumi-dumi: A karshe NAF ta magantu kan harin ta’addanci a sansanin Kaduna
Rundunar sojin sama ta karyata rahoton kai harin ta’addanci a sansaninta na Kaduna Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Facebook

Gabkwet ya bayyana cewa rahoton aikin masu yada labaran karya ne, inda ya kara da cewa babu wani abu makamancin haka.

Ya ci gaba da bayyana cewa mazaunan dukkanin sansanin suna gudanar da ayyukansu na yau da kullun ba tare da wata barazana ba.

Karyane: Sojin Saman Najeriya Sun Karyata Jefa Bama-Bamai Kan Masu Daurin Aure

A wani labarin, rundunar Sojin sama ta Najeriya ta bayyana rahotannin fashewar bam a wurin daurin aure a jihar Neja a matsayin wani yunkuri na bata sunan kokarinsu da sauran Hukumomin Tsaro, The Nation ta ruwaito.

Daraktan Hulda da Jama'a da Watsa Labarai na Sojan Sama na Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, a cikin wata sanarwa, ya musanta batun da cewa:

"Idan da gaske an kai hari kan masu daurin aure, tambayar da ya kamata 'yan Najeriya su yi ita ce 'Me ya sa za a daura aure a wani yankin dazuzzukan da ke da yawaitar ayyukan 'yan bindiga?

Asali: Legit.ng

Online view pixel