Jerin Jami'o'in Tarayyar Najeriya Da Suka Yi Karin Kudin Makaranta

Jerin Jami'o'in Tarayyar Najeriya Da Suka Yi Karin Kudin Makaranta

Bayan gazawar kungiyar da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta yi na matsawa gwamnatin tarayya ta karo kudin kula da jami'o'i, wasu fittatun jami'o'in gwamnati a Najeriya sun kara kudin makaranta.

Da dama cikin jami'o'in kasar sun sanar da karin kudi fiye da kashi 200 cikin dari wurin rajista da kudin makaranta.

Jami'ar Maiduguri
Jerin Jami'o'in Tarayyar Najeriya Da Suka Yi Karin Kudin Makaranta. Hoto: STEFAN HEUNIS/AFP.
Asali: Depositphotos

Ga jerin wasu daga cikin jami'oin tarayyar da suka yi karin kudin makaranta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse

Gwamnatin tarayya ta Dutse, kamar yadda rahotanni suka zo ta yi karin kudin makaranta na zangon karatu na shekarar 2022/2023 cikin takardar da ta fitar a Disamban 2022.

Domin saukakawa iyayen yara biyan kudin, jami'ar ta bada daman yin biya biyu, kashi 60 a zangon karatun farko sai sauran kashi 40 a zango na biyu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojojin Najeriya Sun Halaka Babban Ɗan Ta'adda da Wasu Mayaƙa Sama da 40 a Arewa

Jami'ar Maiduguri (UNIMAID)

Jami'ar Maiduguri ta ce ta yi karin kudin makarantar ne saboda hauhawar farashin kaya a kasar. Ga jerin wasu kudaden da ta yi karin.

  • Sabbin dalibai masu karatun likitanci - N252,500;
  • Sabbin dalibai masu karatun aikin ma'aikatan jinya da Medical Laboratory - N136,500;
  • Sabbin dalibai na Anatomy - 162,500;
  • Sabbin dalibai na Physiotherapy - N131,500; sai sabbin dalibai na Radiography - N133,500
  • Tsaffin dalibai na Faculty of Medical Sciences- daga N122,000 da N258,000.

Gwamnatin Tarayya, Lafia (FuLafia)

Jami'ar Tarayya ta Lafia, Jihar Nasarawa, ita ma an rahoto ta yi karin kudin makaranta ya kai N150,000 ga wasu tsangayan karatun.

Daga cikin su akwai daliban likitanci da za su biya N150,000

Amma, ba a musu karin kudin rajista.

Jami'ar Uyo (UniUyo)

Tsaffin dalibai na Jami'ar Uyo a baya suna biyan N50,000. Amma, yanzu an yi karin kudin zuwa N100,000.

Daga cikinsu, akwai daliban likitanci da za su rika biyan N105,750 yayin tsaffin dalibai za su biya N107,750.

Kara karanta wannan

Karancin Takardun Naira Na Shafar Ramadan, Kungiyar Izala Ta Fada Wa Gwamnatin Buhari

Tsaffin dalibai na tsangayar ilimi za su biya N75,750 yayin da tsaffin dalibai za su biya N77,750.

Jami'ar Noma Ta Micheal Okpara, Umudike

Jami'ar Noma ta Micheal Okpara, Umudike ita ma ta yi karin kudin makaranta, sun ce kudin ayyuka sun karu.

Jami'ar ta sanar da hakan ne a Disamban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel