Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutum 4 da Yan Bindiga Suka Sace Jihar Katsina

Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutum 4 da Yan Bindiga Suka Sace Jihar Katsina

  • Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar ceto wasu mutum huɗu da miyagun ƴan bindiga masu ɗauke da makamai suka yi garkuwa da su
  • Jami'an ƴan sandan rundunar sun ceto mutanen ne a ƙauyen Dankolo cikin ƙaramar hukumar Dandume tare da haɗin gwiwar jami'an sojoji
  • Kakakin rundunar ƴan sandan a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa an miƙa mutanen a hannun ƴan uwansu bayan an kamnala duba lafiyarsu

Jihar Katsina - Jami'an ƴan sanda sun ceto wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Dandume da ke jihar Katsina.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, Abubakar Sadiq-Aliyu, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 28 ga watan Oktoban 2023, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Rayukan Yan Bindiga Masu Yawa Sun Salwanta Bayan Sun Kawo Harin Ramuwar Gayya a Jihar Arewa

Jami'an tsaro sun ceto mutum 4 a Katsina
Jami'an Tsaro sun ceto mutum hudu da aka yi garkuwa da su a Katsina Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

A cikin sanarwar, kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Asabar, tare da haɗin gwiwar sojoji, rahoton TheCable ya tabbatar.

Sadiq-Aliyu ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne a yayin wani sintiri a kewayen ƙauyen Dankolo na ƙaramar hukumar ta Dandume.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“A wani yunƙuri na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ƴan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji sun ceto wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a jihar."
"Yunƙurin da jami'an tsaronmu suka yi da jajircewarsu ya kai ga samun nasara, wanda hakan ya sa aka ceto mutanen.”

Kakakin ƴan sandan ya ce an yi wa wadanda lamarin ya rutsa da su gwajin lafiya domin tabbatar da lafiyarsu, kuma an miƙa su a hannun iyalansu.

Gwamna Dikko ba zai tattauna da yan bindiga ba

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mata Mai Shayarwa da Wasu Mutane Masu Yawa a Jihar Arewa

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta hau teburin sulhu da ƴan bindiga ba.

Gwamnan ya bayyana cewa ko da matarsa aka samu a cikin ƴan bindiga sai ya miƙa a hannun hukumomin da suka dace domin fuskantar hukunci.

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 3 a Katsina

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutum uku a wani mummunan hari da suka kai a ƙauyen Domawa da ke ƙaramar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kuma yi awon gaba da bayin Allah masu yawa waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel