Dillalan Simintin BUA Sun Yi Magana Mako 4 Bayan Rage Farashin Buhu Zuwa N3,500

Dillalan Simintin BUA Sun Yi Magana Mako 4 Bayan Rage Farashin Buhu Zuwa N3,500

  • Wasu dillalan simintin BUA sun bayyana dalilin da ya sa har yanzu farashin simintin bai ragu ba duk da kamfani ya karya farashin
  • Sun bayyana cewa kamfani yana siyar musu da kowane buhu ɗaya kan N3,500 amma jigilarsa zuwa wuraren kasuwanci ya sa ba zasu iya sauke farashin ba
  • A ɓangaren dillalan, suna biyan N1,000 kan kowane buhu ɗaya ga manyan motocin da zasu ɗauko musu kayan

Wasu daga cikin dillalan simintin BUA a jihohin Legas da Ogun sun bayyana dalilin da ya sa har yanzun suke siyar da buhu kan sama da N5,000.

Ƴan kasuwar simintin sun yi wannan ƙarin haske ne makonni huɗu bayan kamfanin BUA ya sanar da karya farashin simintinsa zuwa N3,500 kowane buhu.

Dillalan simintin BUA sun yi magana.
Abinda ya sa har yanzu simintin BUA bai sauka ba Hoto: National Archives
Asali: UGC

Idan baku manta ba, Kamfanin ya karya farashin buhun simintin daga N5,500 zuwa N3,500 daga ranar 2 ga watan Oktoba, 2023.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Murnar Nasarar Tinubu, Babban Jigon APC Ya Rasu a Hatsarin Jirgi a Bayelsa

Bincike ya nuna cewa bayan makonni hudu har yau farashin simintin BUA bai canza ba, kuma har yanzu ana sayar da shi sama da Naira 5,000 a jihohin Legas da Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dillalai sun faɗi inda matsalar take

Jaridar The Cable ta tattaro cewa dillalan siminti sun tabbatar da cewa kamfanin BUA na siyar masu da kowane buhu kan N3,500 a masana'anta da ke Benin.

Amma a cewar 'yan kasuwar simintin, dole sai sun je can Benin sannan za su samu siminti a wannan farashin mai rahusa.

An hakaito wani wakilin BUA na cewa, kamfanin na bukatar karin manyan motoci domin rarraba kayayyakinsa, rahoton Leadership.

Don haka, ya ce ya zama tilas dillalan su dauki hayar babbar mota da zasu biya Naira 1,000 kan kowane buhu, ta kai masu kaya zuwa dakunan ajiyar su.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa Ta Bayyana Dalilin Gwangwaje Yan Majalisu da Motocin N160m Duk da Rashin Kudi a Kasa

Dillalan dai sun ce sun hada kai don daukar hayar manyan motoci, amma Naira 1,000 kan kowane buhu ke kashe musu guiwa, hakan ya sa gara su koma sayar da simintin wasu kamfanonin.

Sun ce daukar hayar manyan motoci daga wasu kamfanoni kamar Dangote na iya haifar da matsaloli kamar kwacewa idan aka kama su da sauransu.

Sun bayyana cewa har yanzu farashin jigilar kayan simintin daga ma'ajiyar kayayyaki zuwa wuraren sayarwa shi ke sa a sayar da shi a kan tsohon farashi.

FG Ta Kaddamar da Motoci Masu Amfani da Iskar Gas

A wani rahoton kuma Domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, gwamnatin tarayya ta fitar da shirin ta na samar da motoci masu amfani da iskar gas (PCNGI).

Wannan shiri ya biyo bayan ƙaddamar da sabbin motocin bas na CNG da za su taimaka wajen rage matsalar sufuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel