Hotuna Sun Bayyana Bayan FG Ta Kaddamar da Motoci Masu Amfani da Iskar Gas

Hotuna Sun Bayyana Bayan FG Ta Kaddamar da Motoci Masu Amfani da Iskar Gas

  • Domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, gwamnatin tarayya ta fitar da shirin ta na samar da motoci masu amfani da iskar gas (PCNGI)
  • Wannan shiri ya biyo bayan ƙaddamar da sabbin motocin bas na CNG da za su taimaka wajen rage matsalar sufuri
  • Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya jagoranci ƙaddamar da taron a fadar gwamnati a ranar Juma’a, 27 ga watan Oktoba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da shirin samar da motoci masu amfani da iskar gas na Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGI), wanda ya ƙunshi kafa cibiyoyi bakwai na sauya motoci a faɗin ƙasar nan.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an gudanar da ƙaddamar da wannan shirin ne a hukumance a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Juma'a 27 ga watan Oktoba, inda shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila ya jagoranci bikin.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Bayyana a Karon Farko Bayan Ya Sha Kashi Hannun Tinubu a Kotun Ƙoli

FG ta kaddamar da motoci masu amfani da iskar gas
Femi Gbajabiamila ya kaddamar da motoci masu amfani da iskar gas Hoto: @abdullahayofel
Asali: Twitter

Zach Adedeji, shugaban kwamitin gudanarwa na shugaban ƙasa na CNG, wanda Mista Farouk Ahmed, babban jami’in hukumar kula da Man Fetur ta NMDPRA, ya wakilta, ya sanar da cewa gwamnati ta cire biyan harajin kan siyan motocin CNG.

Adedeji ya jaddada cewa babban makasudin shine samar da makoma mai ɗorewa ta hanyar amfani da wadataccen makamashin da Najeriya ke da shi, wato iskar gas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana shirin kafa cibiyoyi masu yawa a fadin kasar na sauya motoci zuwa masu amfani da gas, cikin makonni biyu masu zuwa.

Adedeji ya jaddada cewa aiwatar da aikin na CNG ya nuna jajircewar shugaba Bola Tinubu wajen tabbatar da tsaftace muhalli da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.

Ribas ta fara siyan motocin bas na CNG

Daraktan ayyuka na shirin shugaban ƙasa na PCNGI, Injiniya Micheal Oluwagbemi ya bayyana cewa gwamnatocin jihohi da dama sun nuna sha’awar su na saka hannun jari a motocin safa na CNG, inda tuni gwamnatin jihar Ribas ta siya adadi mai yawa domin magance ƙalubalen sufuri a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Sha Kaye a Kotun Ƙoli, Shugaban Matasan PDP Ya Shiga Babbar Matsala

Game da farashin sauya motoci zuwa CNG, Oluwagbemi ya bayyana cewa ya bambanta dangane da samfurin abin hawa da nau'insa.

FG Ta Maka Kungiyoyin Kwadago Kotu

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta maka ƙungiyoyin ƙwadago a kotu kan yin biris da umarnin kotu na hana su shiga yajin aiki.

Gwamnatin tarayya ta ce kotun masana'antu ta bada umurni na hana kungiyoyin kwadago yin zanga-zanga ko yajin aiki kan batun janye tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel