Yadda Ya Kamata a Ladabtar Da Dalibai a Makaranta, Masana Sun Magantu

Yadda Ya Kamata a Ladabtar Da Dalibai a Makaranta, Masana Sun Magantu

A ranar Juma'a 20 ga watan Oktoba ce shugaban makarantar Al-Azhar da wasu malamai su ka rinka dukan wani dalibi har zai da ya rasa ransa a Zaria da ke jihar Kaduna.

Dalibin mai suna Marwan Nuhu Sambo wanda ke aji ukuu a karamar sakandare ya gamu tsautsayin ne saboda ya yi fashin zuwa aji.

Daga bisani, gwamnatin jihar ta rufe makarantar sannan 'yan sanda sun kama shugaba da mataimakin shugaban makarantar kan zargin dukan dalibin.

Masana sun yi bayanin yadda ya kamata a hukunta dalibai a makarantu
Yadda ya kamata a hukunta dalibai a makaramtu. Hoto: Farfesa Tahir Mamman.
Asali: Twitter

Tattaunawar Legit Hausa da wasu masana kan wannan matsalar

Legit Hausa ta tattauna da wani Daraktan makaranta mai zaman kanta da kuma shugaban wata makaranta kan wannan lamari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan wata makaranta mai zaman kanta da bukaci a sakaye sunansa ya soki ladabtar da yara ta wannan tsari inda ya duk da akwai bambancin malamai amma ya kamata su san wane irin hukunci za su yi.

Kara karanta wannan

Birnin Gwari: An Kuma Rasa Mutane da ‘Yan Bindiga Su Ka Kai Hare-Hare a Kaduna

Ya ce:

“Duk abin da dalibi ya aikata bai kamata a masa wannan hukunci ba, amma sam ban a goyon bayan wannan bayan irin wannan hukunci.
“A makarantar da na ke jagoranta mafi yawan malamai na ganin ina fifita dalibai a kansu, amma ba haka ba ne kawai ina tsoron yin hukunci irin wannan ne.
“Ina yawan musu bita kan irin hukuncin da ya dace a yi, misali wuraren da ya kamata a daka sun hada da damtse da hannu da kafa da kuma mazaunai.”

Wane shawara suka bai wa iyayen yara?

Daraktan ya kara da cewa dole iyaye su gane cewa tarbiya ba a makaranta kadai ta ke ba dole a hada hannu don inganta tarbiyar yara.

Ya kara da cewa:

“Ina bai wa iyaye shawara su sani tarbiya sai hada karfi da karfe don makaranta ba wuri ne da za a samu tarbbiya dari bias dari ba ne, saboda ko wane tsuntsu kukan gidansu ya ke yi.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan 'Yan Takara 5 da Jam'iyyun da Za Su Fafata a Zaben Jihar Kogi a Wata Mai Kamawa

“Wasu malamai su na tsayawa su natsu kafin yanke hukunci saboda ko wane malami da yadda ya ke, wani ya na da saurin fushi.”

Shugaban makarantar Alhuda Model School, Abubakar Yunusa ya ce ya kamata malamai su dauka cewa dalibai kamar jarirai su ke.

“Shi dalibi yaro ne da ya zo neman ilimi, amma ko wane yaro ya na zuwa ne da tarbiya daga gida, aksari iyayae ba su dauka duka shi ne hanyar ladabtarwa ba.
“Shi yasa mu ke tafiya kafada da kafada da iyayen yara, wurin shawarwari don sanin hanyar ladabtar da yara ba sai dole duka ba.
“Tabbas ana yin dukan amma sai ta kama, mafi yawanci yara kanana duka yafi tasiri amma lokacin da yara su ka fara balaga, dole malamai su na kula.”

Ya kara da cewa mafi yawan lokuta su na fahimtar da malamai yanayin yadda za a yi duka na dalibai.

Kara karanta wannan

Satar Mazakuta: Menene Gaskiyar Batun Da Ya Zama Ruwan Dare a Sassan Najeriya

A karshe, ya bai wa iyaye shawara kan muhimmancin ilimi inda ce dole su taimakawa makaranta wurin tarbiyan yara tare da hada karfi don inganta rayuwarsu.

‘Yan sanda sun kama shugaban makaranta kan dukan dalibi har lahira

A wani labarin, ‘yan sanda sun cafke shugaban makarantar Al-Azhar da ke Zaria a jihar Kaduna.

Jami’an sun dauki matakin ne bayan shugaban da wasu malamai sun yi wa dalibin JSS 3 dukan tsiya har ya rasa ransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.