Da dumi-dumi: Kotu ta baiwa makasan Janar Alkali beli
Babba kotun jihar Flato ta baiwa wasu mutane bakwai da ake zargi da kisan marigayi Janar Ibrahim Alkali beli.
An gurfanar da su ne da laifin hannu cikin kisan tsohon shugaban gudanarwa hukumar sojin Najeriya, wanda aka hallaka a hanyarsa daga Abuja zuwa Bauchi. Za ku tuna cewa a watan Disamban 2018, kotu ta sake wasu daga cikinsu.
Suna gurfana ne kan laifuka biyar na shirya sharri, kisan kai, kin baiwa jami'an tsaro goyon baya wajen bincike, taruwa domin haddasa fitina da kuma kin barin a nemi gawar marigayin.
A sauraron karan da akayi ranan Laraba, Jastis Daniel Longji, ya baiwa mutanen bakwai beli kan kudi naira miliyan biyar.
Kana kowanne zai kawo mai tsaya masa, kuma wajibi ne mai tsayawan ya ajiye takardan filin mallakansa a jihar Plateau.
Ya daga karar zuwa ranan 16 da 18 ga watan Afrilu, 2019.
KU KARANTA: Yan bindiga sun kaiwa shugaban kamfen Buhari mumunan hari
A baya mun kawo muku cewa alkalin kotun jihar Plateau, Jastis Daniel Longji ya baiwa mutane ashirin da ake zargi da kisan janar Ibrahim Alkali beli a ranan Litinin, 17 ga watan Disamba, 2018.
An damke mutane 28 a watan Oktoba da zargin hannu cikin kisan Janar Idris Alkali wanda aka nema aka rasa a ranan 3 ga watan Satumba yayinda yake tafiya daga Abuja zuwa Bauchi.
Alkalin yace: "Na saurari jawaban lauyoyin kan bukatun beli. Karkashin doka mai lamba 100,138 da 148, zargi na 3, 4 da 5 da ake tuhumarsu dashi na boye gaskiya, kin son a nemi gawar marigayin ya sabawa doka. Amma da aka cajesu a lokacin, da yanzu sun gama zaman kurkuku."
"Amma sauran, bani da lokacin sauraron abubuwan da lauyoyin ke fada saboda takardun da aka kawo na da yawa. Sai na duba su."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng