Kisan Janar Alkali: Rundunar 'yan sanda ta bayyana neman wasu mutane 13 ruwa a jallo
- Rundunar yan sandan Filato jihar Filato ta bayyana neman karin wasu mutane 13 ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu a kisan marigayi Manjo Janar Idris Alkali
- Mai magan da yawun rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP Terna Tyopev, ne ya sanar da hakan yau, Alhamis
- Yace 12 daga cikin mutanen sun fito ne daga kauyen Dwei a yankin masarautar Du, yayin da daya dan asalin garin Gushet-Shen ne dake karamar hukumar Jos ta Kudu
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Filato ta bayyana neman karin wasu mutane 13 ruwa a jallo bisa zarginsu da hannu a kisan marigayi Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya).
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP Terna Tyopev, ne ya sanar da hakan yau, Alhamis, a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Jos, babban birnin jihar Filato.
A cewar Tyopev, 12 daga cikin mutanen sun fito ne daga kauyen Dwei a yankin masarautar Du, yayin da daya dan asalin garin Gushet-Shen ne dake karamar hukumar Jos ta Kudu.
"Bayan gudanar da bincike mai zurfi a kan kisan Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya), mun gano cewar har yanzu akwai wasu mutane 13 dake da hannu a kisan sa da basu shigo hannu ba.
"Saboda haka ne kwamishinan 'yan sanda na jihar Filato, Mista Austin Agbonlahor, ya bayar da umarnin bayyana nemansu ruwa a jallo," a cewar Tyopev.
Tyopev ya lissafa sunayen mutanen kamar haka; Kanan Nyam, Solomon Gyan, Dung Deme, Gynag Murak, Da Chuwang Samuel da Nyam Samuel.
Ragowar sune Dung Gbeh, Daddy Dogo, James Dung, Gynag Dung, Jay Boy da wani Destiny da kuma Gyang, da ba a fadi sunayensu na biyu ba.
A ranar 4 ga watan Nuwamba ne rundunar 'yan sanda a Filato ta gabatar da mutane 19 da ake zargi da hannu a kisan Alkali kuma an gurfanar dasu a gaban kotu washegari kafin daga bisani a tisa keyar su zuwa gidan yari.
An fara sanar da batan Alkali a ranar 3 ga watan Satumba bayan ya bi ta garin Jos a hanyar sa ta zuwa Bauchi daga Abuja a motar sa.
KU KARANTA KUMA: Bamu da wuta a gida, siyan ruwan sha muke yi – Dan Dino Melaye ya koka
A ranar 29 ga watan na Satumba, 2018, ne aka gano motar sa a cikin kududdufi mai zurfi dake yankin Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu.
A ranar 31 ga watan Oktoba ne aka gano gawar sa a cikin wata tsohuwar rijiya a unguwar Gushwet a yankin Shen a karamar hukumar Jos ta kudu.
Hukumar soji ce ta binne gawar marigayin ranar 3 ga watan Nuwamba, 2018, a Abuja.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Leit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng