Da dumi dumi: An kama ‘kanwa uwar gami’ dake da hannu a kisan Janar Idris Alkali

Da dumi dumi: An kama ‘kanwa uwar gami’ dake da hannu a kisan Janar Idris Alkali

Rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da kama gagararren mai laifi wadanda ake zarginsa da hannu cikin kisan tsohon shugaban sha’anin mulki a shelkwatar rundunar Sojan kasa, Manjo Janar Idris Alkali.

Daily Trust ta ruwaito shi dai wannan ‘kanwa uwar gami’ ne bayan daukan tsawon suna bin sawunsa sakamakon cika wandonsa da iska da yayi, kamar yadda lauya mai kara, Joe-Kyari Gadzama SAN ya bayyana ma kotu.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya bayyana manyan kalubalen da ake fuskanta a yaki da ta’addanci

Da dumi dumi: An kama ‘kanwa uwar gami’ dake da hannu a kisan Janar Idris Alkali
Janar Idris Alkali
Asali: Facebook

Lauya Gadzama ya bayyana ma Alkalin babbar kotun jahar Filato dake Jos haka ne a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, inda ya nemi kotun ta bashi dama ya sanya sunan wannan mutumi da ake zargi cikin jerin wadanda ake tuhuma, tare da gudanar da kwaskwarima ga tuhume tuhumen.

A watan Nuwambar shekarar 2019 ne Yansanda suka sanar da cewa akwai mutane biyu da ake zargi da hannu cikin kisan Janar Alkali da suka ranta ana kare, inda rundunar Yansandan ta sanar da sunayensu kamar haka; Chuwang Samuel inkiya “Morinho” da Nyam Samuel inkiya “Soft Touch”.

Bayan sauraron jawabai daga bakunan lauyoyin masu kara da lauyoyin wadanda ake kara, Alkalin kotun, mai sharia Arum Ashom ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 24, 25 da 26 kamar yadda lauya Gadzama ya bukata, tare da fara sauraron karar.

Idan za’a tuna, a ranar 3 ga watan Satumba ne Janar Alkali ya bace bat a garin Jos yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga babban birnin tarayya Abuja, inda daga bisani a ranar 29 ga watan Satumba aka gano motarsa a cikin wani rafi dake garin Dura-Du, a kudancin garin Jos.

Bayan dogon bincike tare da bin diddigi ne aka gano gawarsa a ranar 31 ga watan Oktoba a cikin wani rijiya dake kauyen Guchwet a lardin Shen na karamar hukumar Jos ta kudu, inda a ranar 3 ga watan Nuwamba aka gudanar da jana’izarsa a babban birnin tarayya Abuja.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai dai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng