Mutanen Gari Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Kwato Dabbobi 150 a Jihar Sokoto

Mutanen Gari Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Kwato Dabbobi 150 a Jihar Sokoto

  • Mutanen gari sun sheƙe ɗan bindiga yayin da zai ratsa ta garinsu a yankin ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sakkwato
  • Rahotanni sun bayyana cewa fusatattun mazauna ƙauyen Giyawa sun kuma kwato dabbobi 150 da 'yan ta'addan suka sace
  • A baya-bayan nan, an ce 'yan bindiga sun kashe mutane huɗu tare da yin garkuwa da wasu mutum 18 a ƙauyen

Jihar Sokoto - Fusatattun mazauna ƙauyen Giyawa a yankin ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sakkwato sun tura wani hatsabibin ɗan bindiga zuwa lahira.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa mutanen ƙauyen sun halaka ɗan ta'addan ne da sanyin safiyar ranar Lahadi da ta wuce kuma sun kwato dabbobi 150 da aka sace.

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu.
Mutanen Gari Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Kwato Dabbobi 150 a Jihar Sokoto Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Rahotanni daga bakin mutanen yankin sun nuna cewa mazauna Giyawa sun hana ɗan bindigan wucewa ta garinsu, a hanyarsa ta zuwa dajin Goronyo mai hadari.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Wata Mata Ɗauke da Kwalayen Kayan Laifi Sama da 50 a Filin Jirgin Sama a Jihar Kano

An ce ɗan bindigan ya gudo ne daga ƙauyen Samana da ke ƙaramar hukumar Binji da nufin zuwa mafakarsu a dajin Goronyo, da zai ratsa ta ƙauyen Giyawa ya gamu da ajalinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana cewa a baya-bayan nan, 'yan bindiga sun kashe mutane huɗu, sun yi garkuwa da wasu 18 tare da sace tulin dabbobi a garin Giyawa.

Shin hukumar 'yan sanda ta samu rahoton abin da ya auku?

Yayin da aka tuntuɓi muƙaddashin jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda reshen jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa'i, bai ɗaga ƙiran da aka masa ta wayar tarho ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a samu kakakin hukumar 'yan sandan ba domin jin ta bakinsa kan lamarin a hukumance, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Manoma Masu Yawa

Jihar Sakkwato da maƙociyarta Zamfara na cikin jihohin shiyyar Arewa maso Yamma da suke fama da hare-haren ta'addancin 'yan bindigan daji a ƙasar nan.

NDLEA Ta Kama Wata Mata da Tulin Haramtattun Kwayoyi a Filin Jirgin Kano

A wani rahoton Jami'an hukumar NDLEA sun cafke wata mai suna Bilkisu ɗauke da ƙunshin holar iblis sama da 50 a filin jirgin Aminu Kano.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce an kama matar ne yayin da take shirin kama jirgi zuwa ƙasa mai tsarki ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel