Tattalin Arziki: Naira Ta Shiga Cikin Sahun Kudi Mafi Rashin Daraja a Duk Afrika

Tattalin Arziki: Naira Ta Shiga Cikin Sahun Kudi Mafi Rashin Daraja a Duk Afrika

  • A kasashen da ke Afrika, babu kudin da su ka rasa darajarsu a shekarar nan irin Naira da Kwanza
  • Rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya yi bayani mai tsoratarwa game da tattalin arzikin Najeriya
  • Baya ga Najeriya mai arzikin mai, kudin kasashen Congo, Zambiya, Ghana da Ruwanda sun karye

Abuja - Babban bankin Duniya ya kawo kudin Najeriya na Naira a cikin kudin da darajarsu su ka fi kowane karyewa a Afrika.

The Cable ta ce darajar Naira da kudin Angola watau Kwanza ya na karyewa sosai, sun zama abin Allah-wadai a nahiyar Afrika.

A shekarar 2023, Naira da Kwanza sun rasa kusan 40% na darajarsu a sakamakon dalilai da-dama.

Naira
Naira ta na rage daraja Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Babban bankin ya ce matakin da bankin Najeriya na CBN ya dauka na cire takunkumi wajen kasuwanci ya nakasa Naira.

Kara karanta wannan

Man Fetur Zai Kara Tsada a Gidajen Mai Tun da Farashin Tashoshi Ya Zarce N720

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Larabar nan ne bankin duniyan ya fitar da rahoton kasashen Afrika kamar yadda ya saba yi sau biyu a kowace shekara.

Sauran kudin da su ka karye

Karyewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya da yawan bashi da ake bin Angola ya taimaka wajen karya Kwanga.

Sauran kudin da su ka karye a shekarar nan sun hada da fam na kasar Kudancin Sudan, Burundi Franc (BIF) da Kenyan Shilling.

Sauran kudin da su ka rasa darajarsu sun kunshi: Congolese Franc, Kwaca ta Zambiya, Cedi ta Ghana da kudin Ruwanda.

Sai Najeriya ta rage buga Naira

A rahoton, bankin duniya ya ja-kunnen Najeriya da Ethiopia da su rage yawan buga kudi, abin da masana sun koka a kai a baya.

Wani kuskure da masana su ke zargin kasashen Afrika su na yi sun hada da rashin tsari wajen fito da tsare-tsare da sunan bada tallafi.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Kira Ga Kwankwaso Da Peter Obi Su Hada Kai Da Shi Don Cire Tinubu, Ya Bada Dalili

Bankin ya yi kira ga gwamnatocin nahiyar su yi hattara da tsare-tsaren kudin kasashen waje domin tsare darajar kudin gida.

Har ila yau, an gargadi irinsu Najeriya da Ghana a kan tsadar kaya, wanda hakan ya na da mummunan tasiri a kan tattalin arziki.

Fetur zai iya tashi a Najeriya

An samu karin akalla N70 a kan kudin da ‘yan kasuwa su ke sayen fetur a tashoshi, hakan zai iya jawo kudin litan mai ya sake tashi.

An rahoto Shugaban NOGASA ya na cewa tasoshi da yawa sun bushe kar-kaf, hakan ya nuna fetur ya fara yankewa yanzu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel