Kungiyar MURIC Ta Gargadi Wike Game Da Hadaka Da Isra'ila Kan Harkokin Tsaro

Kungiyar MURIC Ta Gargadi Wike Game Da Hadaka Da Isra'ila Kan Harkokin Tsaro

  • Kungiyar MURIC ta tura gargadi ga Nyesom Wike, ministan Abuja kan alakar da ya ke kullawa da Isra'ila
  • Wike na shirin hada alaka da kasar Isra'ila wurin taimaka masa don inganta tsaro a birnin Tarayyar Nigeria, Abuja
  • MURIC a cikin wata sanarwa ta ce Isra'ila ba abin yarda ba ce a harkar tsaro saboda barazana ce ga kasashen duniya

FCT, Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta gargadi ministan Abuja, Nyesom Wike kan shirin yarjejeniyar tsaro da kasar Isra'ila.

Wike na shirin yin yarjejeniya da masana tsaro a Isra'ila don tabbatar da inganta tsaro a birnin Tarayya Abuja.

MURIC ta gargadi Wike kan shirin alaka da Isra'ila
Kungiyar MURIC Ta Yi Martani Kan Shirin Alakar Wike Da Isra'ila. Hoto: MURIC.
Asali: UGC

Meye MURIC ke gargadin Wike a kai?

Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 5 ga watan Oktoba a Abuja.

Kara karanta wannan

Takardun Tinubu: Atiku Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Ya Ke Yaki Da Bola, Ya Nemi Goyon Baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akintola ya ce martanin Wike akan alaka da Isra'ila abin takaici ne inda ya ce bai kamata a amince da kasar Isra'ila a ko wane dalili ba.

Ya ce ta yaya za a amince da Isra'ila a harkar tsaron Najeriya wacce ita kanta barazana ce ga tsaron kasashen duniya.

Ya ce:

"Kasar Isra'ila ta na tauye hakkin 'yan Adam kuma ba ta daraja sauran addinan mutanen duniya, kuma ba ta amince da kawance da kasashe ba.
"Muna gargadin Najeriya da shirin wannan alaka da Isra'ila wanda zai kara jawo tabarbarewar tsaro ne a Najeriya.
"Wannan hadaka za ta kara rikirkita tsaron Najeriya daga na cikin gida zuwa da kasa da kasa."

Farfesan ya kara da cewa Wike na alaka da Isra'ila ne da tunanin cewa kasar Kiristoci ce kamar yadda Kiristoci a Najeriya su ke tsammani, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Martani Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Ya Ce Babu Adalci A Tsarin, Ya Fadi Dalili

Ya ce wannan tunani na su ba haka ba ne saboda Isra'ila babu addinin da ta yi imani da shi illa Yahudanci wanda akwai hujjoji akan hakan.

MURIC ta soki bambanci addini na Gwamna Adeleke na jihar Osun

A wani labarin, Kungiyar MURIC ta nuna damuwa kan yadda Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya nuna wariya a nadin mukamai.

MURIC ta ce ya tabbata Adeleke na yi wa kungiyar CAN aiki ne a boye ganin yadda ya bayyana kiyayyarsa ga Musulmi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel