Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai 870 a Jihar Kano

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Dauki Nauyin Karatun Dalibai 870 a Jihar Kano

  • Sanata Jibrin Barau ya cigaba da bada tallafi ga daliban jami’o’in da su ka fito daga mazabarsa
  • Dalibai kusan 1500 su ka ci moriyar tallafin Mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar nan
  • Bayan an biya kowane dalibin jami’ar BUK, yanzu ana rabawa daliban YUMSUK kyautar N20, 000

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Jibrin Barau, ya cigaba da daukar dawainiyar wasu daga cikin daliban jihar Kano.

Kamar yadda This Day ta fitar da rahoto, Sanata Jibrin Barau ya soma tallafawa sahu na biyu na daliban mazabarsa da ke karatun digiri a jami’a.

Sanatan ya ba mutanen Arewacin jihar Kano tallafin N20, 000 domin yin karatu a jami’ar nan ta Yusuf Maitama Sule da ake kira North West.

Sanata Barau Jibrin
Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin Hoto: thelabourngr.com
Asali: UGC

Kokarin Sanata Jibrin Barau a kan ilmi

Hadimin ‘dan majalisar, Ismail Mudashir ya shaidawa manema labarai haka jiya a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Aika Ta’aziyya Yayin da Aka Sake Yin Rashin Dattijo a Arewacin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi ya wakilci Sanata Jibrin Barau wajen taron kaddamar da bada tallafin domin a taimakawa ‘yan Kano ta Arewa.

A watan Agusta aka shigo da wannan tsari inda aka taimakawa dalibai 628 da ke jami’ar Bayero.

Rahoton People Daily ya nuna Sanatan ya yi alkawarin taimakon ragowar daliban yankin Arewacin jihar Kano da ke karatu a manyan makarantu.

"Duk wani dalibi zai amfana da N20, 000, albarkacin Sanata Jibrin Barau, kuma duk mutumin Arewacin Kano da ke karatu a Najeriya zai amfana.
Mun fara a watan Agusta da daliban BUK, yau mu na jami’ar YUMSUK a sahu na biyu."

- Barau Jibrin

Yadda tallafin Sanata za su taimaka

Wata daga cikin daliban da ta amfana da wannan kudi, Ummussalam Haruna Yusuf ta godewa mataimakin shugaban majalisar dattawan kasar.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Fadi Dalili 1 Tak Da Zai Sauya Siyasar Kano, Ya Yi Wa 'Yan Kasuwa Alkawari

Malama Ummussalam Yusuf ta ce tallafin za su taimaka masu wajen yin kudin mota zuwa makaranta da kuma cin abinci da dai makamantansu.

Sanata Hanga ya tallafawa dalibai

Kwanakin baya an ji labarin yadda shi kuma Sanata Rufai Hangamai wakiltar Kano ta tsakiya ya dauki nauyin biyawa dalibai kudin karatun jami'a.

'Dan majalisar dattawan ya zabo wasu dalibai da ke karatu a jami’ar Bayero da ke Kano, ya biya masu kudin karatu a sakamakon karin da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel