Hafsan Sojojin Najeriya, Lagbaja Ya Rasu? Rundunar Ta Fitar da Sanarwa kan Lamarin

Hafsan Sojojin Najeriya, Lagbaja Ya Rasu? Rundunar Ta Fitar da Sanarwa kan Lamarin

  • Rundunar sojojin Nigeriya ta musanta labarin da ake yadawa cewa Laftanar-janar Taoreed Lagbaja ya rasu
  • Rundunar ta ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya a cikin labarin da ake yadawa na mutuwar Lagbaja
  • Hakan ya biyo bayan yada wani rahoto da ke cewa Taoreed Lagbaja ya rasu a wani asibiti da ke kasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Nigeriya ta yi martani kan jita-jitar rasuwar hafsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.

Rundunar ta musanta rade-radin da ake cewa, Taoreed Lagbaja ya riga mu gidan gaskiya.

An samu karin bayani kan jita-jitar rasuwar hafsan sojoji, Lagbaja
Rundunar sojoji musanta labarin mutuwar hafsanta, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Sojoji sun ƙaryata jita-jitar mutuwar Lagbaja

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024 a shafin X.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi kokarin da ya yi da yake mulki, ya koka da rashin tsaro a yau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya kan labarin da ake yaɗawa na mutuwar Lagbaja.

Hakan ya biyo bayan yada wani labari a kafofin sadarwa cewa Lagbaja ya rasu sanadin cutar daji.

A cikin sanarwar aka ce Lagbaja ya rasu bayan cutar daji da yake dama da ita ta yi tsanani yayin jinya a kasar ketare.

Har ila yau, rahoton ya ce an boye mutuwar Lagbaja ne saboda wasu manyan sojoji sun fara bin kafa kan mukaminsa.

Karanta labarai masu alaka da sojojin Najeriya

Kara karanta wannan

COAS: Rundunar sojin Najeriya ta nada mukaddashin hafsan sojoji, ta bayyana dalili

Ana jita-jitar hafsan sojoji, Lagbaja ba lafiya

Kun ji cewa rahotanni sun ba da labarin cewa hafsan sojojin Najeriya, Laftanar janar Taoreed Lagbaja yana fama da rashin lafiya.

Hakan ya sanya wasu daga cikin manyan sojoji suka fara bin kafar yan siyasa da masu sarautar gargajiya domin maye gurbinsa.

Sai dai rundunar sojojin ta ƙaryata labarin inda ta ce Lagbaja ya dauki hutu ne kuma babu wata matsala a cikin shugabancinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.