Tashin Hankali Yayin da Aka Kwato Gawar Wata Mata Daga Bakin Jibgegiyar Kada

Tashin Hankali Yayin da Aka Kwato Gawar Wata Mata Daga Bakin Jibgegiyar Kada

  • An ruwaito ydda wata mata ta tsinci kanta a bakin kada, inda daga baya aka ciro gawarta bayan kai ruwa rana
  • Majiya ta ce, an kashe kadar da aka gani dauke da gawar matar, duk da cewa ba a gano musabbabin mutuwarta ba tukuna
  • An yawan samun irin wadannan matsaloli a yankuna daban-daban na Kudu maso Gabashin Amurka, musamman Florida

Jihar Florida, Amurka - Jami’ai sun ce kashe wata kada, inda suka fitar da ita daga kududdufi a jihar Florida ta Amurka tare da ciro gawar wata mata ‘yar shekara 41 a bakinsa.

'Yan sanda sun ce sun yi hakan ne bayan samun rahoton yadda aka ga gawar a cikin kududdufin mai zurfin da bai wuce mita hutu ba., Channels Tv ta tattaro.

Jami’an sun gano gawar ne a ranar Asabar, amma sun ce yanayi da kuma sanadin mutuwar matar bai bayyana ba tukuna, sai an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Murkushe Yan Ta’adda 52, Sun Ceto Mutum 62 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

An kwace gawar wata mata daga bakin kada
An kwace gawar wata mata a bakin kada | Hoto: clemson.edu
Asali: UGC

Wani shaida, Jamarcus Bullard ya shaidawa kafafen yada labaran Amurka cewa ya ga wata katuwar kada da gawa a cikin kududdufin daga nan ya garzaya zuwa wata tashar kashe gobara da ke kusa don kai rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Na jefi kadar da dutse, don ganin ko da gaske akda ce. Ta janye gawar zuwa cikin ruwa."

Bullard ya ce an kai ruwa rana ainun kafin a yi nasarar kaiwa ga kashe kadar da kuma dauko ta daga cikin ruwan, New York Post ta ruwaito.

Yadda aka ciro kadar

An ruwaito cewa, bayan kashe kadar, jami’an sun yi nasarar dauko ta daga cikin ruwan ne ta hanyar daura mata igiya a jiki.

Samun tsaiko daga kadoji ya zama ruwan dare a Kudu maso Gabashin Amurka, musamman a jihar Florida da wannan ya faru.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

A watan Yuli, kada ta kashe wata mata mai shekaru 69 da haihuwa, a wani kududdufi da ke Kudancin Carolina, inda 'yan sanda suka ce dabbar ta tsare jikinta tare da hana kowa tunkarar wurin.

Kada ta cinye kafar wata mata

A wani labarin, an samu yadda wata mata ta rasa kafarta ta dalilin kada da ke rayuwa a ruwa, kamar yadda ta ba da labari.

Wannan lamari dai ya faru ne a Kenya, kasa mai yawan namun daji a nahiyar Afrika, kuma ake yawan samun masu ziyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel